Hukumar rijistar malamai ta Nijeriya, TRCN, ta nuna damuwarta kan karuwar yawan malaman da ba su cancanta ba a kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin babban abin da ke kawo koma baya a fannin ilimi.
Babbar jami’ar gudanarwa ta TRCN, Dokta Ronke Soyombo, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a lokacin da ta bayyana a gidan Talabijin na Channels acikin shirin ‘The Morning Brief’, a bikin ranar malamai ta duniya ta 2025.
Dokta Soyombo ta koka kan yadda mutane da dama da ke koyarwa a makarantu a fadin Nijeriya a halin yanzu ba su cancanta da koyarwa ba don basu da ilimin karantawa yadda ya kamata – lamarin da ya fi kamari a makarantu masu zaman kansu.
“Akwai malamai da yawa da ba su cancanta da koyarwa ba. Muna da masu koyarwa a ajujuwa amma ba su da cancantar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta.
Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da jikinsu da zuciyarsu, amma rashin amintattun shaidar koyarwa a hukumance ke hana basu aikin koyarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp