‘Yan takarar biyu sun zafafa yakin neman zabensu yayin da ya rage ‘yan kwanaki a garzaya rumfunan zaben a ranar Talata don zabar wanda zai gaji Shugaba Joe Biden.
A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyar Republican Donald Trump ya jagoranci wani taron gangami a Dandalin Madison Skuare da ke birnin New York, inda ya fara da jero maganganun masu nasaba da kalaman nuna wariyar launin fata.
- Rungumar Harkar Noma Mafita Ce Ga Ma’aikata Masu Ritaya
- ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-18 Sun Mika Ragamar Aiki Ga Takwarorin Su Na Shenzhou-19
Abokan huldar tsohon shugaban kasar ma su ma sun yi ta furta irin wadannan kalamai kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Trump wanda shahararre ne kuma fitacce a New York a gomman shekaru, yana fatan yin amfani da bikin wanda za’a yi a shahararren wurin nan da aka sani na gudanar da mashahuran wasannin kwallon raga da bukukuwan Billy Joel, domin yin sallama da amayar da cikin shi a fafatawar da zai yi da ‘yar takarar Democrat Kamala Harris, a zaben shugaban kasar, duk da dai rabon da jihar ta marawa wani dan takarar shugaban kasa na Republican baya tun a shekarar 1984.
Wasu daga cikin wadanda suka rika gabatar da jawaban bude taro sun rika yin amfani da kalmomin nuna wariyar launin fata, da kalaman da ba su dace ba wajen zaburar da dandazon wadanda suke hallara a wurin sa’oi kafin Trump ya yi Magana.
Rudy Giuliani, wani wanda ya taba zama magajin garin birnin New York kuma tsohon lauyan Trump, ya yi wa Harris sharrin cewa wai tana bangaren ‘yan ta’adda a fadan da ake yi tsakanin Isra’ila da Palasdinu, yana mai cewa wai tana son kawo Falasdinawa cikin Amurka.
A wani sakon email yakin neman zaben Harris ya ce, taron gangamin Dandalin na Madison Skuare, manuniya ce ga irin hadari da rarrabuwar kawuna da ke kunshe a sakon da Trump din ke aikawa.
A gefe guda, yayin nata yakin neman zaben a ranar Lahadi, Harris ta nemi karfafa wa masu jefa kuri’a a Philadelphia, kwarin gwiwa a yankin wanda jam’iyyar Democrat ke da goyon baya sosai.
Ta nuna muhimmancin fitar masu jefa kuri’a wajen zabe don a rinjayi Trump a yankunan na karkara a Pennsylbania da yake da goyon baya.
A ranar, ta halarci ibada a coci, sannan ta ziyarci wurin aski, shagon sayar da littattafai, gidan cin abinci na kasar Puerto Rico da kuma wurin koyar da kwallon kwando ga matasa.
A lokacin wani taro a karshen rana, Harris ta ce “ba wanda zai zauna a gefe” a wannan zabe.
Ta kuma ce Trump yana mai da hankali ne kawai kan kansa yayin da ita kuma take neman shugabancin kasa domin taimakawa Amurkawa.