Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA) da ke samun tallafin gwamnati, bisa zarginsa da yada labaran son zuciya.
Wani babban jami’in fadar White House ya nakalto a kafar yada labara ta FOd News cewa “Muryar Amurka ba ta bin tafarkin Amurka tsawon shekaru.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta rushe wasu ma’aikatun gwamnati guda bakwai da suka hada da Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta Amurka, ciki har da Muryar Amurka da kuma Rediyon Free Europe/Radio Liberty.
- Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama
- El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
“Za a kawar da abubuwan da ba na doka ba da ayyuka na hukumomin gwamnati domin su zama sun yi daidai da dokar da ta dace, kuma irin wadannan kungiyoyi za su rage ayyukansu domin su kasance suna aiki kamar yadda doka ta bukata,” in ji umarnin zartarwar.
Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta Amurka (USAGM) da babban mai ba ta shawara, Kari Lake, sun ce hukumar “ba za a iya warware matsaloli ba.”
An ba da rahoton cewa, ma’aikatan Muryar Amurka sun sami sanarwar sauye-sauyen ta hanyar imel daga Crystal Thomas, darektan hulda da jama’a na USAGM.
An kuma sanar da ma’aikata masu zaman kansu da ‘yan kwangila na kasa da kasa kan dakatar da ba da tallafi. A lokaci guda kuma, an daina ba da tallafi na tarayya ga gidajen Rediyon ‘Free Asia da Rediyo Free Europe/Radio Liberty’.
Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce shi da kusan dukkan ma’aikatansa 1,300 an ba su hutun biyan albashi biyo bayan umarnin.
Har ila yau, umarnin zartarwa ya shafi wasu hukumomi, ciki har da Ma’aikatar Sasanci da Shiga Tsakani ta Tarayya; Hukumar Yada Labarai ta Duniya ta Amurka; Cibiyar Nazarin Duniya ta Woodrow Wilson, Cibiyar Smithsonian; Cibiyar Gidan Tarihi da Ayyukan Laburare; Majalisar Sadarwar Amurka; Asusun Ci gaban Al’umma na Cibiyoyin Kudi; da Hukumar Bunkasa kananan Kasuwanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp