Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen shirya ganawar kai tsaye da zai jagoranta tsakanin shugaban Rasha Bladimir Putin da takwaransa na Ukraine Bolodymir Zelensky.
Trump wanda ya bayyana fatan cimma wannan nasara a nan kusa, ya bayyana haka ne bayan kammala ganawa da shugabannin manyan kasashen Yammacin Turai da shugaban NATO da kuma shugaba Zelensky a fadar White House.
- Babban Burina A Harkar Fim Shi Ne Ganin Habakar Harshe Da Al’adun Hausa—Murtala Abdullah
- Yadda Ake Alale
Shugaban na Amurka wanda a makon daya gabata ya gana da takwaransa na Rasha Bladimir Putin, ya ce nan bada jimawa ba zai sake shirya wata ganawa da za ta hada Zelensky da Putin wuri guda, don kawo karshen wannan rikici.
Da ya ke tsokaci game da ganawar tasu, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merze, ya ce wannan ganawa da Trump ya fara jagoranta, ta bude kofa game da fatansu na ganin an kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
Shi kuwa a nasa bangaren, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce irin wannan ganawa abu ne mai muhimmanci musamman ga tsaron nahiyar Turai, don haka ya bada shawarar shirya wata ganawa nan gaba tsakanin dukkanin bangarorin da abin ya shafa.
Wasu majiyoyi na kusa da Putin dai sun bayyana cewar, ya na fatan ganawar da za su yi ta gaba da Zelensky da Trump zai jagoranta ta kasance a Mo
scow.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp