Zababban shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce zai sa harajin kashi ashirin da biyar kan dukkan kayan da aka shigar Amurka daga Mexico da Canada a ranar farko ta shugabancinsa.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, zababben shugaban kasar ya ce zai kakaba harajin har zuwa lokacin da Mexico da Canada za su dakatar da shigar da kwayoyi da kuma kwararar baki kasar ta kan iyakokinsu.
- Tinubu Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka
- Trump Ya Gayyaci Mark Zuckerberg Cin Abinci
Mista Trump ya kuma yi alkawarin kara kashi goma kan harajin kayan Chana har ita ma sai ta dakatar da fataucin kwayoyin zuwa Amurka.
Wakilin BBC ya ce a lokacin yakin neman zabensa, Trump ya yi barazanar sanya harajin kashi dari na kayan da ake shigarwa Amurka daga Mexico da Chana madamar ba su yi abun da ya dace ba.
A nata martanin, Chana ta ce tana daukar matakin dakile fataucin miyagun kwayoyi tun bayan yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin Shugaba Biden da takwaransa na Chanar, Di Jinping.
Haka zalika, Donald Trump ya sha alwashin yin amfani da sojojin kasar wajen tasa keyar miliyoyin bakin hauren dake zaune a kasar ba tare da cikakkun takardu ba, shirin da ya sabawa al’adar Amurka ta yin amfani da sojoji a cikin gida.
Sai dai masana shari’a na ganin zai yi wuya a iya kalubalantarta a kotu.
Mashawartan Trump sun ce suna da niyar yin amfani da sojoji wajen gina wuraren tsare bakin hauren da basu da takardun zama ko kuma yin safararsu zuwa wajen Amurka, abin da zai bai wa jami’an tsaron kan iyaka da na kula da shige da fice kariya daga tuhuma ko tsarewa.
Masana na cewa gwamnati na da kariyar doka idan ta takaita rawar da sojojin za su taka zuwa na tallafawa, musamman a kan iyakar Amurka da Mexico, ba tare da sun yi mu’amala da wadanda ake tuhuma ba.
“Ina ganin hakan ba zai fuskanci kalubalen da zai yi nasara ba,” a cewar Ryan Burke, farfesa akan al’amuran da suka shafi aikin soja da dabarun yaki a kwalejin sojin saman Amurka, a jawabinsa na kashin kansa.
“Akwai boyayyun abubuwa da dama a cikin wadannan dokoki da basu fito karara sun ce, kai ba zaka iya aikata haka ba kai tsaye.”
Dokar tabbatar da tsaron al’umma ta 1878 (Posse Comitatus) ta haramta yin amfani da sojojin tarayya wajen aiwatar da doka a cikin kasa.
Majalisa ta yi togaciyar da ta sahalewa shugabannin kasa yin amfani da sojoji wajen tallafawa al’amura irin su yaki da haramtaccen fataucin miyagun kwayoyi da kuma lokutan tarzoma.