Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano yace zai roki shugaban kasa Bola Tinubu ya sa baki domin nemo mafita kan magance matsalar yunwa a jihar.
“Mun san cewa, sauran sassan kasar nan suna fuskantar irin wannan kalubalen, amma jiharmu ce a gabanmu farko,” inji shi.
- APC Ta Lashe Zaɓen Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Kachia/Kagarko A Zaɓen Cike-gurbi
- ADP Ta Doke NNPP, Ta Yi Nasarar Lashe Zaɓen Cike-gurbi Na Mazaɓar Sanatan Filato Ta Arewa
Ya ce lamarin ya yi kamari, don haka dole ne Gwamnatin Tarayya ta sa baki don fitar da jama’a daga halin da ake ciki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan kasuwar jihar a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Litinin.
An kira taron ne a karo na biyu, domin tattauna halin da ake ciki a harkokin kasuwanci, musamman a kan tsadar kayayyaki, da nufin samar da mafita ga matsalar.
Gwamnan ya koka da yadda ake fama da matsalar yunwa a jihar, inda jama’a musamman talakawa ke gaza cin abinci a kalla sau uku a rana.