Daruruwan masu zanga-zangar a jiya sun bijirewa gargadin ‘yansanda inda suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa a sassa daban-daban na birnin Ibadan na jihar Oyo, inda suka yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kawo sauyi cikin gaggawa.
Masu zanga-zangar, wadanda suka mamaye manyan unguwanni a cikin birnin Ibadan a safiyar jiya Litinin da yau Talata, sun bukaci shugaban kasar da ya gaggauta magance matsalolin rashin tsaro, matsalolin tattalin arziki, da yunwa da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
- Kasar Sin Karfi Ce Ta Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
- Bikin Bazara Na Shekarar Dabbar Loong Ya Baiwa Duniya Damar Ganin Muhimmancin Tattalin Arzikin Sin
Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwarsu kan tsadar rayuwa, lamarin da suka ce yana kawo wa jama’a wahala wajen biyan bukatun rayuwa.
Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro da suka hada da sace-sacen mutane, da fashi da makami, da hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, masu zanga-zangar sun nufi Sango, Jami’ar Ibadan, amma ana kyautata zaton cewa za su kawo karshen zanga-zangar a sakatariyar gwamnatin jihar da ke Agodi, Ibadan.