A daidai lokacin da al’umma Nijeriya ke fama da hauhawar farashin kayyakin abinci da tsadar rayuwa, sanannen malamin addinin nan na Jihar Kano, Sheikh Mujajjadina Sani Kano, wanda kuma shi ne shugaban masu ilimin taurari na Afirka, ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakan gwamnati da su gaggauta daukar matakin kawo wa mutane saukin matsin rayuwar da suke fuskanta in har suna son kauce wa fushin Allah (SWT).
Sheikh Muhajjadina ya yi wannan bayanin ne a hirarsa da manema labarai a garin Kano ranar Talata. Ya kuma kara da cewa, halin da mutaten ke ciki da matsin rayuwa ya wuce duk yadda ake tunani. “Lamarin a halin yanzu ya kai matsayin Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun”. Ya ce, babu wani bangare na rayuwar al’umma da ba su dandan wannan halin da ake ciki. A kan haka malaman addini musulmunci da na addnin Kirista suka hadu a yin kira ga gwamnati ta samar wa al’umma mafita.
- ‘Yan Boko Haram Sun Sake Lalata Layukan Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
- Muna Kara Kira Da Ayi Gwajin Kwayoyi Kafin Yin Aure – Marwa
Shehin malamin wanda shi ne shugaban Gidauniyar (Muhajjadina Humanitarian Foundation) wadda ta shahara wajen tallafa wa al’umma, ya kara da cewa, a kullum suna samun mutane masu neman taimako maza da mata da marayu masu lalulori daban-daban., “ Yanzu kusan kowa ka gani a hanya yana bukatar taimako” in ji shi.
Ya kuma ce, mataki mai muhimmanci da ya kamata gwamnati ta dauka don kawo karshen matsalar tsadar rayuwa shi ne dawo da tallafin man fetur da wannan gwamnatin ta janye a farkon kama mulkinta Ya ce, man fetur ya shafi dukkan bangarorin rauwar al’umma, janye shi ya haifar da tsadar rayuwa. Kuma gashi darajar naira na kara faduwa a kullum, “In har gwamnati ta dawo da wadannan abubuwan biyu to da yardar Allah abubuwa za su yi sauki” in ji shi.
Daga nan Shekih Muhajjadina ya yi gargadin cewa, in har gwamnati ba ta dauki matakin kawo wa al’umma saukin rayuwa ba, to lallai za su gamu da fushin Allah (SWT). “Allah na iya kwace mulkin ya ba wadanda za su taimaka wa mutane” in ji shi.
Ya kuma nemi gwamnati a dukkan mataki su nemi shawarwarin malaman addini wajen gudanar da harkokinsu, musamman abin da ya shafi raba wa al’umma tallafi, “Domin daga cikin malamai ne ake da tabbacin samun masu tsoron Allah, wadanda za su jagoranci raba wsa mutane abin da aka tanada, ya kuma kamata a cire duk wani na’u’i na siyasa a wajen bayar da tallafi, domin yunwa bai san banbanci a tsakanin dan APC ko dan PDP ba” in ji shi.