Mambobin Majalisar Wakilai, sun amince su rage kashi 50 cikin 100 na albashinsu na tsawon watanni 6 don sadaukarwa da tallafawa kan rage matsalolin tattalin arziki da yunwa da ‘yan Nijeriya ke fama da su a halin yanzu.
Hakan ya biyo bayan amincewa da wata bukata da mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu ya gabatar kan bukatar ‘yan majalisar su sadaukar da kashi 50 na albashin su na Naira 600,000 duk wata don tallafawa Gwamnatin tarayya wajen shirin shawo kan kalubalen tsadar rayuwa da ake fama da shi a kasar.
- Kamfanin Sin Ya Fitar Da Sabon Nau’in Karafan Kafafun Jiragen Kasa Masu Saurin Tafiya
- Ko Kun San Miliyan Nawa Gombe Ke Kashewa Don Tsaftace Jihar A Duk Wata?
Bukatar da Kalu ya shigar, ta biyo bayan kudirin da dan majalisa Isiaka Ayokunle ya gabatar na yin kira ga masu goyon bayan zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar da su yi watsi da shirin, wanda a nata bangaren, majalisar ta yanke shawarar taimakawa gwamnati da albashinta.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce, za a yi amfani da albashin da suka rage ne domin tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya na magance tsadar kayan abinci a kasar da nufin magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ta hanyar rage albashin ‘yan majalisun da kashi 50 cikin 100, ‘yan majalisar su 360 za su rika sadaukar da Naira miliyan 108 duk wata na tsawon watanni shida masu zuwa.