Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ɗorewar tsaftar muhalli da manufofin ƙarfafa al’umma su rungumi al’adar tsafta a Jihar Zamfara.
A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da rabon motoci da kayayyakin aiki daban-daban na shirin Tsaftar Muhalli na Matasan Zamfara a gidan gwamnati da ke Gusau.
- Trump Zai Fuskanci Tirjiya A Duniya, Ba Soyayya Ba – Shehu Sani
- Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa rabon kayayyakin wani babban tsari ne na shirin Tsaftace Jihar Zamfara, wanda ya haɗa da manyan motocin kwasar shara guda goma, injinan shara guda huɗu, manyan motoci guda biyu, da babura 65.
Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin na ‘Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes’ (ACReSAL) ya samar da kwandon shara guda 450 na ma’aikatun gwamnati da kuma kwandon shara na ƙarfe 55 ga al’ummomin birane.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa tsaftataccen muhalli yana jawo jari, da bunƙasa harkokin yawon buɗe ido, da inganta rayuwar al’ummar jihar Zamfara baki ɗaya.
“Wannan taron ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarinmu na ceto jihar Zamfara cikin watanni 20 da suka gabata.
“Shirin ƙarfafa matasa na Zamfara an yi shi ne don ƙarfafa matasanmu masu kuzari da hazaƙa ta hanyar shigar da su cikin ayyuka masu ma’ana don inganta tsaftar muhalli a faɗin jihar.
“Wannan shiri ya wuce inganta tsaftar muhalli kaɗai; yana ba da guraben ayyukan yi da haɓaka dabarun kasuwanci. Muna fatan cewa ta hanyar shiga cikin waɗannan shirye-shirye, matasanmu za su sami ƙwarewa sosai da kuma fahimtar alhakin hidimta wa al’umma.
“Ta hanyar shirin ZAYOSAP, muna kuma saka hannun jari a makomar matasanmu. Muna ba su kayan aiki masu muhimmanci da ilimin da zai shirya su don zama shugabanni da wakilai wajen kawo sauyi a al’ummominsu. Wannan cikakkiyar dabara ta ƙarfafa matasa da ɗorewar muhalli ba shakka za ta haifar da fa’ida ga jiharmu.
“Yayin da muke ƙaddamar da wannan shirin a yau, mun kafa tarihi ne ga al’umma masu zuwa. Ina fata wannan shiri zai zama abin koyi ga wasu jihohi uku da zaburar da saura wajen ƙirƙirar irin wannan shiri a faɗin Nijeriya.
“A bayyane yake cewa yayin da muke gina muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar, tsaftar muhalli na da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar rayuwar al’umma da kuma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Tsaftace tituna, kasuwanni, da wuraren jama’a suna nuna kimar al’umma a idon duniya. Ina kira ga masu ruwa da tsaki da suka haɗa da shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya, da ɗaukacin al’ummarmu da su goyi bayan wannan shiri ta hanyar rungumar al’adar tsafta.
“Da waɗannan kalamai, nake farin cikin ƙaddamar da shirin tallafa wa matasan Zamfara a hukumance. Ina kira ga al’ummar jiharmu da su bai wa wannan shiri goyon baya tare da haɗa kai domin cimma burin jihar Zamfara na tsafta, lafiya da wadata.”