Kwanan nan, rikicin da ya barke na cacar baki tsakanin hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote da mahukuntan bangaren mai na Nijeriya ya dauki hankali sosai a manyan gidajen jaridu da sauran kafofin sadarwa har da na sada zumunta.
Saboda mamakin abin, ‘yan Nijeriya masu kishi sun shiga rudani a kan rikicin. Da farko, attajirin ya zargi Kamfanonin Mai na Waje da ke aiki a Nijeriya da yi wa sabuwar matatarsa zagon kasa ta hanyar hana su samun danyen man da ake hakowa a Nijeriya da rahusa. Sai ma ya zama, yadda za a sayar wa wasu a waje ya fi nashi sauki, inda shi aka kara masa farashin daga dala 4 zuwa dala 6 a kan kowace ganga.
- Majalisa Ta Nemi A Kori Shugaban Hukumar NMDPRA Kan Zargin Rashin Ingancin Matatar Dangote
- Duk Da Sulhu, Tsugune Ba Ta Kare Ba Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Mai
Uhum! In ji mai ciwon hakori. Cikakken Dan Nijeriya, ya kafa matatar mai a kasarsa ta gado amma an ki sayar masa da man kasarsa don ya tace ya sayar wa da ‘yan kasarsa. Wace irin kasa ce wannan? Kuma maimakon mahukuntan da abin ya shafa su nemi hanyoyin daidaita lamarin, sai suka zama masu mara baya ga kamfanonin na waje har ma suka fi su tsanantawa ta hanyar kushe sabuwar matatar man wacce babu irin ta kaf Afirka, alhali kuma sun ki gyara na kasa da ake da su guda uku a Kaduna, Warri da Fatakwal duk da makudan biliyoyin da aka narka.
Lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin mai, ya yi alkawari wa ‘yan kwadago cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Disambar 2023. Aka ce ba a kammala aiki ba, amma a watan Janairun 2024 za ta fara, da watan ya zo ya shige sai aka kuma cewa babu shakka a watan Afrilu za ta fara, amma mai karatu har yau shiru kamar Malam ya ci shirwa. Kuma wani dan kasuwa shi kadai, ya bugi kirji, ya yi abin da kasar ta kasa yi, amma sai aka rika bin sa da tsangwama da hantara.
Kamar yadda na ji wani mai hikima yana jawabi a wani faifan bidiyo da na gani yana yawo a shafukan sada zumunta yana cewa, Nijeriya ta kasance tana sayar da danyen mai a kasashen waje daga nan sai ta sayo tataccen mai daga can. A yanzu kuma da aka samu matatar mai ta Dangote, sai aka hana matatar man isasshen danyen mai da za ta tace, don haka sai aka kuma garzayawa waje don shigo da danyen mai wadda daga bisani bayan tacewa za a kuma fitarwa zuwa waje. Wannan wane irin kwance zani ne a kasuwa?
A duk kasashen Afira, kasashe biyu ne rak ba su shigo da tataccen mai daga waje. Daga Aljeriya sai Libiya, sannan kusan an kwashe shekara 20 kasar Angola tana fafutukar kafa babbar matatar mai abin bai yiwu ba, haka nan ita ma Yuganda ta kwashe shekaru 15, duk dai bai yiwu ba. To, mu me ya sa da namu ya yi maimakon a yaba sai aka koma bita-da-kulli?
Matatar man Dangote abar alfahari ce ga Nijeriya a tsakanin sa’o’inta na duniya. Saboda tun daga zayyanarta har zuwa gina ta da sanya na’urorin aiki komai a Nijeriya aka yi. Na ji cewa, Dangote ya yi wa katafaren gine-gine da ake ganin babu kamarsa a Nijeriya na Julius Berger tayin aikin amma kamfanin ya ce ba shi da kayan aikin da zai iya kwangilar. Dole ta sa Dangoten da kansa ya niki gari ya bazama neman kayan aikinsa da kansa kuma ya yi amfani da injiniyoyi na cikin gida masu yawa wajen aikin ginawa.
Kamar yadda mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Mista Edwin ya tabbatar, wannan ne karon farko da aka samu katafariyar matatar mai da za ta tace ganga 650,000 a kullum da aka hada kwangilar sauton kayan aiki da kawo su da kuma gina su a lokaci guda a duk fadin duniya kuma irin ta, ta uku da ta hade sassan matatar mai a wuri daya a duk fadin duniya. Wannan kadai bai ishe mu alfahari ba? Sannan Bisa kayan aikin da aka shigo da su na gina matatar, Dangote ya ce babu wani aikin gini da zai iya gagarar Nijeriya a halin yanzu.
Shugaban Hukumar Daidata Al’amuran Mai ta Kasa, Injiniya Faruk Ahmed ya yi zargin Dangote yana yunkuri ne na yin babakere a harkar man Nijeriya, to amma Dangoten ya ba shi amsar cewa, “ba mu taba ko da darsawa a zuciya cewa, mu hana wani yin kasuwancin da muke yi ba. Duk wanda zai yi ai ga fili ga doki.”
Kuma ma don Allah, don dan kasa ya gina wani abu na samun kudi a kasarsa ta gado mene ne na kyashi? Ai da arziki a garin wasu gwara a naku. Amma a wurin shugabannin mai na Nijeriya gwara a bai wa turawan yamma. Shi ya sa wani ya ce, “da zarar wani ya yi maka bayani a game da yadda za ka fahimci Nijeriya, bayan ya kammala sai ka ce ka gane, to tabbas bai yi maka bayani yadda ya kamata ba ne,” ma’ana, duk yadda aka kai ga yi maka bayani, za ka rasa INA MUKA DOSA?