Ya zuwa wannan shekara, cinikin tsakanin Amurka da Afirka na dogaro ne da dokar AGOA matuka, saboda wannan doka ta bai wa kayayyaki kirar Afirka damar shiga kasuwannin Amurka ba tare da biya harajin kwastam ba. Amma yadda shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fara kakkaba wa kasashen da ke huldar ciniki da kasarsa karin haraji, ciki har da kasashen Afirka 51 ka iya haifar da kalubale ga kasuwancin Afirka na fitar da kayayyakinsu zuwa Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Rueters ya ba da labari a kwanan baya cewa, manazarta na ganin cewa, dokar AGOA wadda wa’adinta zai kare a watan Satumba mai zuwa na fuskantar kalubalen daina aiki. Kasashen Afirka na fahimtar wannan matsala, inda ministar masana’antu da ciniki da zuba jari ta Najeriya Dr. Jumoke Oduwole ta bayyana a cikin wata sanarwar cewa, “Ko da yake man fetur ya kasance albarkatu mafi muhimmanci da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka, amma akwai wasu kayayyaki da ba na man fetur ba da aka yafe musu haraji bisa dokar AGOA wadda, wadanda kuma za su fuskanci matsala”.
- Inganta Kiwon Lafiya: Gwamna Buni Ya Ziyarci Sabuwar Cibiyar Sayar Da Magunguna Da Ke Damaturu
- Yawan Wutar Lantarki Da Kasar Sin Ke Iya Samarwa Ya Karu Da Kaso 14.6% Zuwa Karshen Maris Na Bana
Amma kasashen Afirka ba za su zauna kawai sun yi asara bisa wannan yanayi na maras tabbaci ba.
Nahiyar dake da yawan mutane fiye da biliyan 1.4 na da babbar kasuwa. Matakin Donald Trump ka iya samar wa kasashen nahiyar damar karfafa hadin gwiwarsu da inganta tsarin masana’antu. Ban da wannan kuma, kasashen Afirka suna iya samun mafita ta hanyar kara hadin gwiwa da kasashe masu tasowa musamman ma kasar Sin.
Cikin shekaru 16 a jere ne Sin take kan matsayin abokiyar ciniki mafi girma ga Afirka. A maimakon matakin da Amurka ke dauka wato kara dora wa kasashen Afirka haraji, Sin tana dukufa kan taka rawar gani cikin tsarin hadin gwiwar mabambantan bangarori da gaggauta hadin gwiwar kasashe masu tasowa da cin moriya tare, matakin da zai samar da yanayi mai dorewa ga bunkasarsu baki daya.
Kazalika, ba kamar yadda Amurka ta kakkaba wa kasashen Afirka harajin da yawansa ya kai tsakanin 10% zuwa 50% ba, Sin ta soke dukkan harajin kwastam ne a kan kasashen da suka fi koma baya wadanda suka kulla dangantakar diflomasiyya tsakaninsu da Sin, ciki har da wasu kasashen Afirka 33, matakin da ya samar wa Afirka damammaki masu kyau wajen more manyan kasuwannin Sin.
Muna iya gani daga wadannan alkaluma cewa: Wane ne ya dunkula hannu kuma wane ne ya bude hannun runguma?, Wane ne ya kafa shingaye kuma wane ne ya gina gada? Girman kai da matukar son kai na zubar da mutumcin da kimar Amurka, yayin da kuma a maimakon haka, kuma matakin bude kofa da hadin gwiwa da Sin ke dauka na kara bayyana nagartaccen mutumci da martabar kasar. (MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp