Hausawa suna da wani karin magana mai ban sha’awa da ke kara shaja’antar da mazumunta a kan kara dankon zumunci a tsakaninsu, shi ne “zumunta a kafa take”.
Yayin da sabuwar shekarar 2025 ta fara lulawa, kasar Sin ta fara sauke hakkinta na yaukaka zumunci a tsakaninta da nahiyar Afirka ta hanyar fara ziyarar ministan harkokinta na waje, Wang Yi a wasu kasashe hudu na nahiyar da suka hada da Namibia, Jamhuriyar Kongo, Chadi da kuma Nijeriya.
- An Kashe ’Yan Ta’adda 34 Da Sojoji 6 A Harin Borno – Shalkwatar Tsaro
- Éric Chelle Ya Zama Sabon Kocin Super Eagles
Ziyarar ta kasance wani bangare na fara shirye-shiryen aiwatar da tsare-tsare 10 da Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi wa nahiyar Afirka albishir da su a taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, watau FOCAC da ya gudana a birnin Beijing a watan Satumban bara.
Sin da Afirka sun yanke shawarar daga matsayin dangantakarsu zuwa kololuwa da za ta karade dukkan fannoni na ci gaba a sabon zamani. Wannan zumunci yana ci gaba da haifar da da mai ido saboda yadda ake gudanar da harkoki a karkashinsa bisa gaskiya da amana ba tare da kumbiya-kumbiya ba. Inda hakan ya taimaka ga raya ababen more rayuwa a Afirka.
Cikin shekaru 25 da suka gabata kacal, kamfanonin kasar Sin da suka zuba jari a nahiyar Afirka sun taimaka wa kasashen yankin da ginawa ko kara inganta sufurin jirgin kasa da ya kunshi layukan dogo fiye da kilomita 10,000, da manyan tituna da tsawonsu ya kai kusan kilomita 100,000, da gina manyan gadoji kimanin 1,000, baya ga tasoshin jiragen ruwa ciki har da masu zurfin ruwa da adadinsu ya kai 100, kana da habaka samar da wutar lantarki ta hanyar gina tasoshin janyowa da layukan rarrabawa da a kalla za su kai tsawon kilomita 66,000.
Kasar Sin ta kuma himmatu wajen tallafa wa Afirka wajen gina masana’antu da za su rika sarrafa ko san’anta kayayyaki a cikin gida domin taimaka wa habakar tattalin arzikin yankin. Haka nan a bangaren ci gaban kimiyya da fasaha da aiki da sabbin makamashi marasa gurbata muhalli, kana bangaren aikin gona ma ba a bar shi a baya ba.
A tsakanin shekarun da ba su wuce 10 ba, kasar Sin ta gina cibiyoyin inganta fasahar aikin gona guda 24 a sassan Afirka tare da habaka fasahohin aikin gona daban-daban fiye da 300 wanda hakan ya taimaka gaya ga samun girbi mai albarka da a kalla kashi 30 zuwa 60 cikin dari inda manoma kimanin miliyan daya suka ci gajiyar abin.
Irin wannan zumunci ake so ya dawwama ana sadar da shi saboda kamar yadda Hausawa kan ce “na ji dadi shi ne batu, ba na saba ba!”(Abdulrazaq Yahuza Jere)