Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin dake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da matsalar da ke addabar wasu ‘yan matan na rashin amincewar soyayyar da suke yi wa samarin da suka gani suke so, musamman idan aka yi duba da irin zamanin da ake ciki wanda ya sauya, sabanin lokutan baya da aka san ‘ya’ya mata da kunya da yakana wajen iya furta kalmar so ga wanda suke so, har sai idan shi namijin ne ya furta wa mace da kansa. Sai dai kuma a yanzu rayuwar ta sauya sabanin irin ta zamanin iyaye da kakanni, domin kuwa da yawan ‘yan mata a yanzu su ne suke kai wa samari tayin soyayyarsu wanda kuma hakan ke sakawa su tsinci kansu cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin amincewar wanda suka yi wa tayin soyayyar.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin matasa game da wannan batu; Wacce soyayya ce ta fi karko bayan an yi aure, tsakanin soyayyar da namiji ne da kansa ya furta wa mace yana sonta da kuma wacce ita macen ce da kanta ta je ta furta wa saurayi cewar tana son sa?, Ko kin taba ce wa namiji kina son sa ba tare da shi ya furta miki ba?, ko ka taba cin karo da macen da ta taba cewa tana son ka kai tsaye ba tare da kai kana son ta ba, wace amsa ka ba ta? Ya soyayyar ta kasance a tsakani ko kuma ya aka taushi zuciyar me son?, Ko ta wacce hanya za a shawo matsalar da ke damun ‘yan mata musamman wadanda suka fada cikin irin soyayyar samarin da suka ki amincewa da soyayyarsu?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Khadija Muhammad Sha’aban, Daga Jihar Kano:
Gaskiya soyayyar da tafi karko ita ce, ta namijin da ya ce yana son mace, amman idan har ki ka sake ki ka auri wanda ke ki ka ce kina son shi, maza suna da wani hali guda daya na wulakanta mace, ko ba-dade ko ba-jima sai ya gaya miki maganar da za ki dade kina jin ta a rai. Idan ki ka auri namijin da ke ki ka ce kina son shi, ba lallai ya dinga girmamaki a matsayin masoyiyarsa ba, saboda zai dinga dubawa ke ki ka kawo masa tallan kanki, zai fi dacewa ki auri wanda ya tako da kansa ya nuna miki kauna har gida. Ban taba cewa ina son kowa ba, saboda a rayuwata ba na son wulakanci. Hanya daya ce kawai ki kama kanki, ki daina bayyana soyayyarki ga wanda kin san ba lallai ya so ki ba, dan wani ma zai iya kasancewa yana sonki, amman ganin kin furta masa kalmar soyayya ya mayar da ke kwallonsa. Shawarar da zan bawa samari da ‘yan’mata ita ce; idan har ta furta maka kalmar so, ko da baka sonta kar ka wulakanta ta, kawai ka bi duk hanyar da za ka bi ku rabu lafiya, ke kuma ‘yar’uwa idan har ya kasance dole sai kin furta masa ba za ki iya tausar zuciyarki ba, to ki san wanda za ki furtawa kalmar so, domin mutuncinki shi yafi miki komai a rayuwa.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya duk kaninsu ana samun dacewa idan saurayin da budurwa sun san matsayin auren a musulunci da kuma martaba ta dan’Adam, domin a lokuta da dama ko da babu soyayya a tsakanin saurayi da budurwa idan Allah ya kaddara faruwar auren za ka ga suna mutunta juna. To magana ta gaskiya a lokuta da dama idan mace ta furtawa namiji Kalmar so to indai ka ga namijin ya amince har an kai ga aure to dama yana so, amma muddun baya son ta ba zai amince ba har a kai ga batun aure ba, domin maza basu cika boye soyayya ba ko kiyayya ba. Eh! hakika hakan yana faruwa sosai ma yanzu ,kuma hakan ba laifi ba ne, muddun tayi zabi nagari ba wai hangen abun duniya ba. To ni ina ganin wannan ba matsala ba ce, domin babu yadda za a yi idan mace ba tada wani saurayin data rike wani ya zo gurin taki karbar soyayyar sa, don haka muddun ka ga mace taki karbar soyayyar mutum to tana da wani wanda take so. To shawara ta anan ita ce ya kamata mutum ya duba daidai da ajinsa idan ya tashi neman auren, kuma ya karbi shawarar da manzon Allah ya bada wajen neman auren domin samun mace ta gari da miji nagari.
Sunana Mariya Sani Usman, Daga Jihar Kano:
Kp mace ta ce tana son namiji ko Namiji ya ce yana son mace indai aka yi aure dole ke made ke za ki fi hakuri, sabida ke mace ke ce a kasan miji, dole ki bashi kwanciyar hankali da nutsuwa. Na taba cewa ina son wani amma wallahi ban samu wani kalubale ba, dan wallahi yana masifar sona kamar daman can shi ya ce yana sona. Shawara hanya daya ce; ki dage da addu’a kuma ya kasance don Allah ki ke son shi Allah zai baki nasara. Ku kuma maza dan Allah ku tausayawa mata duk kunya irin ta mace har ta cire ta nuna tana sonku dan Allah ku tausayawa mata in kuma yarinyar bata yi muku ba dan Allah kar a ce ba a sonta a lallashe ta saboda abin da tayi sunnah ce. ‘Yan’uwana mata kar ku yi nauyi da kwauron baki, wallahi duk namiji da ki ka ga ya yi miki za ki iya rayuwar ki da shi ki yi masa magana kar ki ji tsoro tunda ke ce za ki nemawa.kanki abokin zama tunda duk yadda ki ke baki yi ya Nana Khadija ba to ki fada in sha Allah za ki yi nasara. ina kara kira ga maza dan Allah duk.macen da ta zo muku da kalmar so dan Allah kar ta zama abar wulakantawa, dan wallahi ta fi wadda ka je ka ce kana son ta da kanka dan ta fi sonka dan Allah a bata dama ka ga irin son.
Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:
Da farko dai gaskiya yanzu yanayi, ko zamani ya canja, komai ba irin na shekarun da suka shude a baya ba ne, da sai in ce soyayyar dukkanninsu biyun suna iya yin kargo, domin shi Namiji a tsarinsa duk abin da zuciyarsa ta darsu da sonsa, to yana bashi mahimmanci sosai, kuma yana iya jure dukan ruwa da iska domin ya ga ya cimma burinsa, wanda hakan zai sa riritawa za ta shigo ciki, kuma hakuri ma da duk wani irin halaye da take yi masa zai shigo ciki har kuma ka ga aure yayi karko. Domin kawai saboda shi ya gani ya ke son abinsa, sabanin a ce zaba masa ita a ka yi, to fa sai abin da ta gani ita ma. Haka ita ma ‘ya Mace matukar tana son namiji, to za ta iya jure duk nau’in wahala da ta zauna da shi, amma idan bata sonsa koda shi mawadaci ne, zai wahala auren yayi karko. Tun da ita ‘ya Mace ta dauki soyayya ne a matsayin rayuwarta, duk wani buri, da cimma muradi tana zuba shi ne akanta ne. Kuma shawarar da zan bawa ‘yan’mata, da samari ita ce: Dukkansu su ji tsoron Allah, su daina tozarta junansu, don wani ya ce yana son wani, soyayya jigon rayuwar mu ce, duk Saurayi ko Budurwa da daya zai furtawa daya neman kulla alakar soyayya, to hakan fa ya nuna Amincewa da, yarda ce, wanda duk ba a samunsu a wurin kowanne irin nau’in mutum ba tare da wani dalili mai karfi ba.
Sunana Hafsat Sa’id Daga Jihar Neja:
Tsakanin soyayya da namiji da soyayyar ‘ya mace bayan an yi aure, a gaskiya soyayyar da namiji tafi karko dalili kuwa idan har mace ce ta ce tana son shi idan aka yi auren babu irin kalar wulakanci da macen ba za ta gani ba, wanda zai iya janyo wa ma ya sake ta, ita za ta iya ci gaba da hakuri da shi amma shi ba zai iya dauka ba. Haka idan shi ya ce yana son macen duk wulakancin da za ta yi masa zai iya shanyewa sabida shi yake sonta. Gaskiya ni dai ban taba cewa ina son namiji ba duk son da nake yi masa na gwammace na barshi a cikin kokon zuciyata saboda idan baka furta ba ma ya ta kare bare kuma ka furta, in ka furta ma wulakanci za ka ga ni, kuma kai ba kai ne a ransa ba, dan haka duk abin da nake so ga da namiji na fi so ya furta mun da kanshi kowane irin so nake yi masa zan iya dannewa zuciyata in yi hakuri. Shawarar da zan bawa matan da suka tsinci kansu a irin haka su daurewa zuciyarsu su hada da addu’a su yi ta hakuri cikin kankanin lokaci za su ga Allah ya futar musi da wannan son dake cikin zuciyarsu.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori A Jihar Jigawa:
Gaskiyar magana a zance mafi inganci soyayyar da ta fi inganci ita ce wacce mace za ta furta cewa tana sonka, domin idan har ka ga mace ta furta wa namiji kalmar soyayya to, gaskiya ta bi dukkanin wasu hanyoyi dan ankarar da shi idan abun yaci tura, shi ne za ta yanke wannan hukunci na karshe, kuma idan aka yi hakan aka ci sa a suka karbi soyayyar juna, idan ka duba za ka ga suna rayuwar su cikin kwanciyar hankali ba tare da ana jin kansu ba, koda daya ya yi wa daya ba daidai ba su kan ba sa jimiri wajen sulhunta kansu tun kafin wani a gefe ma ya ji abun dake wakana, domin gudun kar ayi musu dariya ko gori musamman a gidajensu misali; idan an kai ruwa rana kafin yin auren. Kuma ki sani ‘yar’uwa cewa kina son namiji ba kashi ba ne, idan har kin gamsu da taunuwar sa da tarbiyyar sa, kuma ina tabbatar miki ba zai wulakanta ki ba, idan kuwa har aka samu akasin hakan ta faru ya wulakanta ki, to ki kyaleshi daman wulakantacce ne. Idan kuma muka yi duba da daya bangaren na soyayyar da namiji ya kan je ya samu mace ya ce yana sonta, wanda wannan auren shi ne mafi shahara musamman a wannan zamani da muke ciki. Yawancin irin wannan auren za ka ga bai cika armashi ba bayan an yi shi, saboda yadda muka tsinci kanmu a wannan zamani wasu matan su kan amince da soyayyar ka ne domin sun rasa wanda zai zo gun su ne, shi ya sa ta amince da soyayyar ka. Daga bisani bayan an yi aure sai ka ga abubuwa suna ta tabarbarewa daga bisani auren ba zai je ko’ina ba tunda ba soyayya ba ce ta kwarai. Shwarar da zan bawa samari musamman wadanda Allah ya jarabce su da soyayyar wata a zuciyar su, ita kuma taki amincewa, Ita ce ka yi hakuri ka roki Allah ya cire maka santa a cikin zuciyarka ka kuma datse dukkanin wani abu da ya shafi mu’amala da ita ka je ka duba wata, domin hakan shi ne mafi alheri a gare ka. Ya kai dan’uwa kada ka kuskura mace ta furta ba ta sonka ka kuma tsaya bata lokacinka na cewa wai nan gaba za su soka ka na yaudarar kanka ne, domin kuwa koda an yi auren wallahi kuskure zai ta afkuwa ba fata ake yi ba. Haka kuma kema ‘yar’uwa idan ki kai wa da namiji tayin soyayyar ki yaki karba to ki yi hakuri ki roki Allah ya yi miki zabi mafi alheri, gudun kar ayi kitso da kwarkwata ko kuma nama ya dahu romo danye.
Sunana Hassana Hussain Malami (Haseenan Masoya) Daga Jihar Kano:
Gaskiya tom wani sa’ilin koda mace ta furtawa namiji tana son shi ba shi yake kawo wulakanci ba a gurin wanda yabsan darajar kansa, sannan kuma idan zai yi koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam ba zai yi mata wulakanci ba, domin shi ma fiyayyen halitta matarsa ta farko ita ta ce tana son sa. Ban taba furta Ina son mutum ba koda ina son sa sai dai zan dungi nuna masa alamu har mu shaku idan soyayya ta kullu shikkenan in kuma ba ta kullu ba shikkenan. Idan ya kasance kin kamu da son wani kuma shi baya sonki mafi a’ala ki bawa zuciyar ki hakuri, sannan kuma ki dagye da addu’a da istahara idan shi alkhairi ne tom da kansa zai furta miki komai ya daidai ta idan hakan bai faru ba kuma ki fawwalawa Allah ba alkhairin ki bane. Ni dai Ina bawa mata shawara idan kin ga wanda ki ke so kafin ki furta masa ki fara istahara.
Sunana Abdulrahman Alhassan Bununu A Jihar Bauchi:
Gaskiya soyayyar da mace ta ce tana sonka zai fi karko badan komai ba sai dan karfin son da take yi wa wanda take kauna hakan na nufin ko a zaman aure ba za ta taba kauce wa umurninsa ba, sabila da son da take yi masa. Kuma indai mace ta soka to, ta mallaka maka dukkan zuciyarta ne mace akan abun da take so takan sadaukar da komai inta wannan shi ne. Dalilina kuwa shi ne Annabi (SAW) da kansa matarsa ummuna Nana Khadija (R.A) ta aure shi sabila da gaskiya da amanarsa wanda in za mu duba sarakuna da manyan masu kudi da suka neme ta amma ta ce a’a. In muka duba yadda zamansu ya kasance abun koyi a gare mu duk da dama manzon Allah (S.A.W) dole duk wanda ta ganshi ko ta ji labarinsa ta kware masa. Tabbas akwai wacce ta taba cewa tana sona duk da cewa ba wai ni ina sonta bane, amma abun da nayi shi ne na bi hanyoyi daban-daban dan na fahimtar da ita da kuma tausasa zuciyarta a haka har muka zama kamar ‘yan’uwa na kan bata shawara game da wani abun duk da ba wai son ne ta daina ba, amma dai nayi nasarar rarrashin zuciyarta. Eh! gaskiya ita ce ‘yan’uwa masoya ko irin wannan matsalar ta faru mu saka wa kanmu hakuri sabila da ba wai in babu shi ko babu ita shi ne ba za mu iya rayuwa ba amma duk da abun da ciwo, amma duk ciyonsa hakuri magani ne da kuma addu’a. shawarata anan ita ce; ‘yan’mata da samari kafin ka furta ko ki furta ki tsaya ki yi nazari ko kuma akwai dabarun da ake yi na dan tsokana a cewa mutum nawance ko na wane anan akan samu amsa yana so ko a’a ko kuma tana so ko ita ma a’a.
Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:
Duba ga mu kasar hausa muke, kuma an san mata da alkunya. Yawancin mu kasar hausa abin ya zama kamar wani al’ada ne namiji ke fara furta yana so sannan mace ta amsa. Hakan ta sa wasu mazan basa bawa matan da suke fara furta suna so daraja. Gaskiya ban taba furtawa wani namiji ina sonsa ba. Duk da musulunci bai haramta hakan ba. Amma gaskiya ni ba zan iya gayawa namiji ina son sa ba. Yawancin matan dake fara nuna suna son namiji suna fuskantar wulakanci daga bisani, da an dan samu matsala kadan kya ji gori, “ai dama ba ni na fara nuna ina sanki ba, dama can ke ki ka nuna kina sona ba ni ba” Ya wanci gaskiya suna daukar hakan ‘for granted’ ne. Ni dai bani da shawarar da zan bayar, amma ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan nasara. Na gode sosai.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Daga Jihar Kano Rano:
Ni namiji ne amma na fi ganin wadda mace ita da kanta ta ce tana so. dalilina na farko shi ne; ita macen ita ta gani ta ce talaka mai kudi ne sai dai kuma ana samun wasu mazan suna fakewa da hakan su yi wa mace wulakanci bayan auren. Dalilina na biyu shi ne; ita kanta macen za ta fi baka kulawa sabida gudun afkuwar wani abin da zai haifar da matsala wadda har iyaye da ‘yan’uwa su zo suna cewa ai dama ita ta gani ta ce tana so da sauransu. Maganar gaskiya akwai su domin akwai wadanda ma muka yi aure sannan yanzu akwai wacce in sha Allahu za mu kai ga auren junanmu kuma na ga amfanin a fara furta cewa ana son naka. Shawara ga samari su ji tsoron Allah suna tausaya musu domin akwai radadi da rashin dadi kace kana so aki ka, kuma ‘yan’mata shawarata a nan ita ce duk fa wanda ya ce yana sonka tofa yana sonka ne ba kada wanda za ka yi alfahari da shi bayan iyaye indai akan mutane ne. Shawarata ita ce don Allah duk wanda ya tsinci kansa ko ta tsinci kanta da irin wannan kada su cutar da dayansu.