Ganin yadda aka yi hasashen za a fuskanci tsananin rana da zafi a yayin aikin hajjin bana, hukumar aikin hajji ta Saudiya ta fito da wani lema na musamman da alhazai za su yi amfani da shi domin kare kansu daga rana da zafi.
Sabon leman na da aljihun ajiye wasu kananan kaya na bukata ya na kuma bayar da kariya na musamman daga hasken rana da ka iya cutar da Alhaji, ana kuma makalawa ne a kai ba tare da an rike da hannu ba.
- Sanusi II Ya Bar Ribas, Bayan ‘Labarin LEADERSHIP’ Na Sake Naɗa Shi Sarkin Kano
- Jami’ai Sun Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Karkashin Dandalin FOCAC
Ma’aikatar aikin Hajji da Umara ta kuma ce, lemar na da saukin sarrafawa ana kuma iya sallah da shi ba tare da wata mastala ba.
“Lemar za ta taimaka wa alhazai gudanar da aikin Hajji cikin natsuwa, musamman ganin tsananin ranar da za a yi a lokacin Hajin bana” in ji sanarwar.
Lema kuma na da aljihun da za a iya ajiye wasu kananan abubuwan amfani kamar ruwa, wayar hannu da sauransu, ana kuma iya yin sujada da shi ba tare da an cire ba.