Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa Darakta-Janar na yakin neman zabensa, Doyin Okupe, kan badakalar kudade ba zai karya kudurinsa na zama shugaban Nijeriya a 2023 ba.
Obi ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), a Uyo, sakatariyar kungiyar da ke Jihar Akwa Ibom a ranar Litinin.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Bude Sabon Babin Aiwatar Da Dokokin Kundin Tsarin Mulkin Kasar A Sabon Zamani
- An Amince Da Kudurin Aiki Na Kunming-Montreal Game Da Kare Mabambantan Halittu Yayin Taron COP15
Tsohon gwamnan na Jihar Anambra, ya ce hukuncin bai taka kara ya karya ba, kuma zai ba da damar bin doka da oda don gudanar da aikinsa.
Obi ya ce, “Ina jin labarinsa [hukuncin Okupe] kamar ku. Har yanzu ina nazarin abin da ke fitowa daga kotun. Na yi imani da bin doka. Ba zai bata min rai ba.
“A rayuwata, ban taba tsayawa a inda aka jefe ni ba, idan ba haka ba, da na kasance inda suka jefe ni a baya. Wannan zaben, idan sun ga dama, to su yi wani abu game da mutanen da ke kusa da ni. Zan kai ga nsara.”
Leadership Hausa ta rawaito cewa an samu Okupe da laifi 26 cikin 59 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), ke tuhumarsa.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayar da umarnin a gudanar da tuhume-tuhume 26, wadanda suka janyo masa zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu kowane.