Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (TUC), wacce hadakar manyan kungiyoyin ma’aikata daban-daban ce a Nijeriya, ta bai wa Gwamnonin Jihar Gombe da na Bauchi, Muhammadu Inuwa Yahaya da Bala Muhammad lambobin yabo ta ‘Gwamnoni Masu Kaunar Ma’aikata’ bisa la’akari da kyawawan manufofi da jajircewar su na inganta aikin gwamnati.
An bai wa Gwamnonin lambar yabon ce yayin wata liyafar cin abincin dare da kungiyar ta TUC ta kasa ta shirya a babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja kwanaki kamar yadda hadiman Gwamnonin, Kwamared Mukhtar M. Gidado, da Alhaji Ismaila Uba Misilli na gwamnan Bauchi da Gombe bi da bi suka fitar a wata sanarwa daban-daban.
A cewar shugaban kungiyar ta TUC na kasa, Kwamared Festus Osifo, an karrama Gwamna Inuwan ne duba da yadda gwamnatinsa take gaggawar biyan albashin ma’aikata da fansho tare da biyan basussukan kudaden giratuti da gwamnatocin baya suka ki biya a jihar, da kuma sauran manufofin dake daɗaɗawa ma’aikata.
Haka zancen yake ga gwamnan Bauchi, inda kungiyar ta ce, tun hawan kujerar gwamnan Bala Mohammed ya shagaltu domin lalibo bakin zaren magance matsalolin da ma’aikata ke fuskata tare da saukaka musu yanayin aiki mai inganci, biyan albashi a kan kari da rage basuka giratuti da fansho da tsoffin ma’aikata ke bi.
A yayin bikin, Gwamna Inuwa ya samu wakilcin mataimakin sa ne Dr Mannasah Daniel Jatau, yayin da shi Kuma na jihar Bauchi, ya samu wakilcin Muhammad Auwal Jatau, mataimakin gwamnan Jihar (zababbe) inda suka amshi lambar yabon a madadin Gwamnonin.
Da ya ke jawabi a madadin gwamnan Gonbe, Dr. Manassah Jatau ya gode wa shugabannin kungiyar ta TUC bisa karramawar, wacce ya bayyana a matsayin kalubale na ƙara jajircewa.
Ya ce, “Bai wa mutum lambar yabo tamkar an kalubalance shi ne; don haka duk wadanda aka bai wa lambar yabo a yau, to fa an kalubalance su ne su kara kokari. Mun karbi wannan kalubalen da hannu bibbiyu don cika muradun kungiyar TUC da ma na ma’aikata baki daya”.
Shi ma Jatau ya ce, lambar yabon da aka bai wa gwamna Bala Muhammad ba ta zo musu da mamaki ba domin yadda suka ga gwamnan ya tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansa da kyautata rayuwar al’umma, hade da zama gwamnan da ke kaunar cigaban aiki a kowani lokaci.
Wakilan Gwamnonin suka ce: “Kofofin mu za su ci gaba da kasancewa a bude ga kungiyar TUC, kuma za mu ci gaba da bada goyon bayan mu a kodayaushe ga TUC da ma’aikata don samar musu kyakkywan yanayin aiki don gudanar da ayyukan su cikin lumana da kwanciyar hankali”.
“Gwamnatocinmu ta ma’aikata ce. A kullum muna bai wa jin dadi da walwalan ma’aikatan jihohinmu muhimmanci a manufofin mu na ci gaba, ciki har da sake fasali da farfado da tsarin aikin gwamnati, da biyan albashi da fansho akan kari, dana biyan bashin kudaden fansho da na sallaman ma’aikata wato giratuti wadda gwamnatocin baya suka gaza biya kamar dai yadda shugabannin kungiyar ta TUC suka bada shaida”.
Taron ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da gwamnonin jihohin Edo da Bauchi, da Rivers da kuma Nasarawa wadanda suka samu wakilci, da Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Kasa NNPC Limited Mele Kolo Kyari, da Sarkin Dass da shugabannin kungiyoyin ƙwadago da jami’an diflomasiyya da shugabannin kamfanoni da dai sauran su.