Ana gudanar da taron shugabannin BRICS karo na 16 a Kazan na kasar Rasha. Wannan taro ya kasance irinsa na farko bayan da BRICS ya shigo da sabbin mambobi 5 a farkon wannan shekara. Daga wani tsari mai kunshe da mambobi 4 zuwa mai mambobi 10, me ya sa BRICS ta samu karin karbuwa a duniya?
Da farko, manufar tsarin BRICS shi ne yin hakuri da juna da hadin gwiwa don neman samun bunkasuwa mai dorewa tare, da kara azama kan kafa duniya dake da madogarai da dama da ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya. A halin yanzu, ra’ayin babakere da yakin cacar baka ya kawowa burin tabbatar da bunkasuwar duniya mai wadata cikin hadin gwiwa cikas sosai, sai dai a nasa bangare, tsarin BRICS ya dace da bukatun yawancin kasashe, wato yin hakuri da juna da samun bunkasuwa tare, kuma ya dace da muradun jama’ar kasashe masu tasowa.
- An Kaddamar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Rasha a Kazan
- Za Mu Fara Kamen Mabarata A Abuja – Wike
Na biyu, an cimma ainihin sakamako karkashin BRICS. Ba kafa bankin raya kasashen BRICS da asusun gaggawa na BRICS kadai aka yi ba, har ma mambobin BRICS sun kai ga matsaya daya kan hadin kansu a bangaren allurar rigakafi da aikin noma da tsarin makamashi da sauransu, ta yadda za a amfanawa al’ummomin mambobinsu. Musamman ma a bangaren tattalin arzikin yanar gizo da tattalin arzikin bola jari, wanda ya kasance muradu na bai daya na kasashe masu tasowa.BRICS ya samar da wani dandalin samun bunkasuwa tare da cin moriya tare, shi ya sa karin kasashe ke neman shiga wannan tsari.
Na karshe, tsarin bunkasuwar BRICS na jawo hankalin kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa. Suna fatan fahimtar dabaru da hanyoyin da Sin take bi wajen zamanintar da al’ummarta, tare da neman cimma matsaya daya a karkashin tsarin BRICS, don kara hadin kansu da inganta karfin hadin kansu ta yadda za su cimma moriya tare da samun bunkasuwa tare.
Bayan habakar tsarin BRICS, yawan al’ummar da BRICS ya shafa ya kai rabin al’ummar duniya, kana yawan cinikin da ya shafa ya kai kashi 1 bisa 5 na duniya. Ganin yadda ra’ayin yin hakuri da juna da samun bunkasuwa da moriya tare na BRICS ke kara samun karbuwa tsakanin mutanen duniya, ya kan ba mutum imanin cewa, tabbas karin kasashe masu tasowa za su shiga wannan tsari don neman samun bunkasuwa a hadin gwiwarsu. (Mai zane da rubutu: MINA)