Zauren tattaunawar tattalin arziki da cinikayya na kawancen BRICS, wanda majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta karbi bakoncinsa, ya gabatar da “Tsarin aiwatar da shirin raya cinikayya da hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS na shekarar 2025-2026” ga bainar jama’a a jiya.
Babban burin wannan shirin shi ne rage shingaye masu wuyar sha’ani da kuma inganta samar da kayayyaki, da ayyuka, da bin al’adu, da karfafa cinikayyar fasahohin zamani tsakanin kasashen kawancen na BRICS ta hanyar daidaita sahu mai inganci da karfafa fahimtar juna.
A wajen taron zauren, wakilai daga kasashe da dama sun bayyana cewa, tsarin hadin gwiwa na BRICS ya zama muhimmin dandali na hadin kan kasashen duniya da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Sun kuma ce, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen BRICS zai yi tsayin daka wajen nuna turjiya a kan shingayen kasuwanci tare da cimma gagarumar nasarar gudanar da harkokin cinikayya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp