ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
7 months ago
Namadi

Gwamnan Jihar Jigawa State,Mallam Umar Namadi, ya yi watsi da maganar gamyyar jam’iyyun adawa,inda yake cewa babu wani abin damuwa kan lamarin kafa ita gamayyar jam’iyyar adawar kafin babban zaben shekarar 2027.A wata hirar da ya Jaridar LEADERSHIP ta ranar Lahadi,yayi karin bayanin cewar maganar da ake cewa farinjinin na ja baya a Arewa ba maganar da za a saurara bace.

 

Amsa kan muradai sha biyu da ya bayyana lokacin da ya fara aiki a matsayin gwamnan Jigawa, ya bada amsar cewa ‘’Mun fara aiki a matsayinmu na gwamnati da burin da muke son cimmawa da kuma manufarmu domin bunkasa Jihar Jigawa ta samu babban ci gaba. Don haka ne muka bullo da muradai goma sha biyu wadanda suka kunshi dukkan bangarori,da suka hada da ilimi,harkar lafiya,tallafawa matasa su dogara da kansu, aikin gona,bangaren tsaro kudaden shiga, bunkasa kauyuka da kuma abubuwan more rayuwa. Bani ne ya dace na ce na yi wa kaina Alkalanci ba,wato ko mun yi abinda za a yabe mu ko akasin haka.Al’ummar Jigawa ne ya dace su yi Alkalanci kanmu.Amma kuma a namu auna ayyukanmu a matsayinmu na gwamnati,ina ganin mun samu ci gaba muna kuma alfahari da irin ci gaban da muka samu.Mun godewa Allah akan damar da ya bamu muka yi abinda ya bamu ikon yi.

ADVERTISEMENT
  • Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe
  • Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

Muna tafiya da al’ummarmu a duk tsare-tsaren da muke yi.Ina da tabbacin cewar Jigawa ita kadai ce Jiha daya wadda take tafiya da al’ummarta a cikin ayyukan da take yi.Yadda muke shirya abin shi ne muna zuwa kowace karamar Hukuma inda muke taro da masu ruwa da tsaki, da dukkan wakilai kowace mazabar Kansilolin kowace Lahadi muna fada masu a matsayinmu na gwamnati, ayyukan da muka yi a shekaru biyun da suka gabata. Suna iya amincewa ko kuma su yi watsi da lamarin. A kowane bangare Kwamishina ne yake yin magana da mutanen kan ayyukan da muka yi. Tun da muna amfani ne da tsarin gwamnatin tarayya,muna cewa kowane Sanata da kuma dan majalisar Wakilai ya fadawa abubuwan da gwamnatin tarayya tayi masu ta hannunsu ‘yan majalisar.

 

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.

 

Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar manoma ne. Duk wata gwamnatin da take bukatar bunkasa tattali arzikin Jigawa da kuma jin dadin zamantakewar al’ummarta dole ne ta maida hankali kan aikin noma. Fannin akin noma shi yake samar da kashi 46 cikin 100 kudaden shiga na gwamnati a shekara.Ina farin ciki na fadi hakan cewar abinda muke yi yayi matukar bunkasa tattalin arzikin Jihar Jigawa, Gaskiya daukar matakin yin hakan ko shakka babu ya bunkasa jin dadin rayuwra al’ummarmu. Maganar gaskiya tsarin ya rage yawan wadanda suke zuwa Birane daga Kauyuka a cikin Jihar. Matasa yanzu sun amince da harkar noma ita ce babbar lamarin kasuwanci amma ba irin noman da mutum zai noma saboda shi kadai ba.Shi yasa muka bada muhimmanci da maida hankali kan noma da komawa gona.

Shi kuma ilimi wani babban ginshikin ci gaban rayuwa ne, ta kowane al’umma na duniya,amma ba sai Jihar Jigawa kawai ba.Shi,yasa muke ganin da akwai muhimmanci da kuma bukatar mu ilimantar da al’ummar mu, saboda kuwa mun san da zarar mun ilimantar da su, musamman ma matasa,wadanda sune za su kasance Shugabannin gobe. Shi yasa lamarin ilimi ma shi ma muka bashi muhimmanci. Domin ai muna da tsare tsaren na lamarin daya shafi ilimin. A babban bangaren ilimin, mun kaddamar da tsarin da ya shafi kafar sadarwa ta zamani a ilmance,ba,abin ya tsaya a samar da ilimi ga al’ummar ba,abin ma yana taimaka mana kan lamarin rashin zuwa aiki na Malaman makaranta.

Bugu da kari an amfana da shi wajen horon su Malaman.Zuwa yanzu,mun haorar da fiye da Malaman makaranta12,a karkashin shi tsarin.

Hakanan ma mun bullo da tsari na rage yawan yaran da basu zuwa makaranta, shi yasa ma muka bullo da tsarin Tsangaya, saboda kuwa Hukuma ce wadda ta fara aiki.Abinda muke yi shi ne mu tabbatar da duk yara a Jihar Jigawa,wadanda basu zuwa makaranta, an dawo da su makaranta.Mun samu nasrara yin hakan.Tsarin Tsangaya ya amince da masu ruwa da tsaki za a koyar da abubuwa uku:lamarin kirga da kuma yakar jahilci na kwana biyu,ilimin addii na kwana uku,sai kuma ilimin koyon sana’a na kwana daya.Tsarin makaranta na Tsangaya zai bada dukkannin abubuwan da suka zama dole wadanda kuma za su taimakawa masu karatu wajen samar da ilimin fasaha da kuma koyon sana’oi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.