Kungiyar masu jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta bayar da “Rahoton ci gaban da aka samu a tsarin samar da kayayyaki na masana’antar lantarki (2025)”, a wajen babban taron kula da yanayin masana’antar lantarki karo na 3 a yau Alhamis.
A cewar rahoton, masana’antar lantarki ta kasar ta bunkasa cikin sauri a ’yan shekarun nan, kana tsarin samar da kayayyaki na masana’antar lantarki ya kara samun karfin juriya.
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wani Yaro Ɗan shekara 2 A Yobe
- NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya
Bisa rahoton, an ce, a karkashin hanzarta bunkasa kasuwa da manufar “Cikakken Tsarin Shiri” da kasar ta gudanar, bunkasar da masana’antar lantarki ke samu na kara kiyaye kyakkyawan ci gaba. A shekarar 2024, adadin kudin masana’antar samar da kayayyakin lantarki ya kai kimanin yuan tiriliyan 21.59, wanda ya karu da kashi 6.1 bisa dari bisa na makamancin lokacin a shekarar 2023, tare da inganta ci gaban bayanai da kididdiga, da bukatun kasuwa a kan kayayyakin lantarki da mutane ke bukata, da kayayyakin lantarki na kera motoci wadanda duka sun kasance masu karfi tare da karfafa masana’antar don ci gaba da samun bunkasa.
Bugu da kari, idan an lura da yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki, yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin a shekarar 2024 ya kai kusan 42000, wanda ya karu da kusan kashi 9 bisa dari a shekarar 2023.
A farkon rabin wannan shekara, masana’antar lantarki ta kasar ta ci gaba da kiyaye ingantaccen yanayin ci gaba. Kudaden shiga da manyan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki suka samu ya kai yuan triliyan 8.04, wadanda suka karu da kashi 9.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Safiyah Ma)