Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian, ya maida martani game da kalaman babban magatakardan kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, a yau Talata 9 ga wata, inda ya jaddada cewa, tsaro da NATO ta sha magana a kai, ya dogara ne kan salwantar tsaron sauran mutane, abun da ya haifar da babban hadari ga duk fadin duniya da ma shiyya-shiyya.
Rahotanni sun ruwaito cewa, a wajen taron manema labarai da aka shirya kafin taron kolin kungiyar NATO, Stoltenberg ya ce, daya daga cikin taken taron kolin shi ne, dangantakar abokantaka tsakanin NATO da sauran sassan kasa da kasa, kana, NATO din za ta tattauna tare da kasashen Australiya da Koriya ta Kudu da Japan da New Zealand kan fadada hadin-gwiwa kan batun Ukraine da sauran wasu batutuwa.
- Liu Guozhong Ya Halarci Bikin Bude Taron Dandalin Hadin Gwiwar Gwamnatocin Kananan Hukumomin Sin Da Afrika
- Li Qiang Ya Taya Keir Starmer Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Birtaniya
Lin Jian ya kuma jaddada cewa, Sin tana adawa da irin abun da NATO ta yi, na shafa mata bakin fenti, gami da dora mata laifi ba gaira ba dalili, da fakewa da batun kasar Sin wajen shiga cikin harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik da gurgunta halin da ake ciki a yankin.
Kaza lika, wata sanarwa dake karkashin jagorancin cibiyar kula da tsaron intanet ta kasar Australiya ta ce, wani mai satar bayanai ta intanet mai suna APT40, ya kai farmaki sau da dama kan gwamnatocin yankin tekun Indiya da Pasifik, alamarin da ya samu amincewa daga kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da New Zealand. Game da wannan batu, Lin Jian ya ce, wasu kasashe sun sake rura wutar rikicin dake cewa, wai kasar Sin ta kai farmaki ta kafar intanet, tare da bata sunan kasar bisa hujjar tsaron intanet, yana mai cewa wannan abun ne da bangaren Sin ke adawa da shi matuka. (Murtala Zhang)