• English
  • Business News
Monday, July 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Bai Wa Sojoji Haɗin Kai 

by Hussein Yero and Sulaiman
5 months ago
in Labarai
0
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Bai Wa Sojoji Haɗin Kai 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙara haɗa kai da sojojin da ke aiki a jihar.

A ranar Alhamis ne gwamnan ya karɓi baƙuncin Babban Hafsan Sojin Sama Air Marshal Hassan Bala Abubakar a ziyarar aiki da ya kai jihar Zamfara.

  • Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
  • Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara 

Babban Hafsan sojin saman ya ziyarci Zamfara ne dangane da harin kuskure da aka kai wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula 11 a kusa da Gidan Makera a Ƙaramar Hukumar Zurmi a ranar 11 ga watan Janairun 2025.

Fararen hular da suka rasa rayukansu ‘yan sintiri na yankin ne waɗanda aka yi kuskure ana zaton cewa ‘yan bindiga ne suka tsere daga farmakin da rundunar sojin sama ta Operation Fansar Yamma ta kai.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da yadda rundunar sojin saman ta ɗauki matakin gaggawa kan kiraye-kirayen da ake yi a yankunan da ke fama da rikici a faɗin jihar Zamfara.

Labarai Masu Nasaba

An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari

Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja

Gwamna Lawal

“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban.

“Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman.

Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da babban hafsan sojin sama bisa gudunmawar da rundunar ta bayar. Suna amsa kiran gaggawa a duk lokacin da muka buƙata.

“Mun fito ƙarara game da matsayinmu. Mun sanar da duk mai saurare cewa ba mu shirya ba kuma ba za mu taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba. Kowa na iya tabbatar da cewa matsayinmu yana samun sakamako, domin mun fara ganin sakamako mai kyau, sannu a hankali zaman lafiya ya dawo Zamfara.

“Ina so in yi amfani da wannan damar in sanar da Air Marshal cewa muna gina filin jirgin sama a Zamfara. Ina roƙon cewa da zarar an kammala filin jirgin, muna son hangar sojojin sama don tabbatar da kowa ya tafi daidai a jihar.

Gwamna Lawal

“Za mu ci gaba da tuntubar ku saboda muna buƙatar sojojin sama. Ba za mu iya gode maka a a kan wannan ziyarar ba. A gare mu a Zamfara, mun jinjina wa wannan tattaki da ku ka yi tun daga Abuja. Daga bangarenmu, ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da yin cudanya da ku, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don tallafa wa sojojin da ke yaƙi da ’yan bindiga. Ina yi muku fatan sauka lafiya a Abuja.”

A farko, Babban Hafsan Sojin sama Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya miƙa godiyarsa ga gwamna Dauda Lawal bisa haɗin kan da ya bayar wajen faɗakar da al’umma kan harin da aka kai bisa kuskure a Zamfara.

“Idan za ku iya tunawa a ranar 11 ga watan Junairu, 2025, an kai hare-hare ta sama a Zamfara sakamakon rahoton sirri na ‘yan bindiga a Gidan Makera a ƙaramar hukumar Maradun. An kai harin ne da nufin fatattakar ‘yan ta’addan da ke da alaƙa da ɗan fashin daji Bello Turji. Kwanaki kaɗan bayan harin, wani rahoto ya yi ikirarin cewa jirgin ya kai harin ne kan wasu ‘yan ƙungiyar ‘yan sintiri bisa kuskure.

“Saboda damuwa da wannan zargi, nan da nan na kafa kwamitin bincike kan harin. Tuni dai kwamitin binciken ya gabatar da rahotonsa da sakamakon binciken, wanda ya tabbatar da cewa an kashe ‘yan sintiri 11 ba da gangan ba.

“Ziyarar mu ta safiyar yau mun yi ta ne don jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, da kuma al’ummar Zamfara bisa wannan mummunan lamari.”

Gwamnan da hafsan sojin sama sun yi wata ganawar sirri da iyalan waɗanda harin jirgin ya rutsa da su, tare da wasu 11 da suka jikkata.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai

Next Post

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai

Related

An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari
Labarai

An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari

3 hours ago
Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja
Manyan Labarai

Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja

4 hours ago
Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015
Kasashen Ketare

Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015

5 hours ago
Ƴan Bindiga Sun Tafka Gagarumar Sata A Bauchi, Sun Tafi Da Mutane 4
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Tafka Gagarumar Sata A Bauchi, Sun Tafi Da Mutane 4

7 hours ago
Yadda Gwamnan Katsina Ya Tsira Daga Hatsarin Mota
Manyan Labarai

Yadda Gwamnan Katsina Ya Tsira Daga Hatsarin Mota

8 hours ago
Saurayi Ya Kashe Budurwarsa, Yace Sharrin Ƙwaya Ne
Manyan Labarai

Saurayi Ya Kashe Budurwarsa, Yace Sharrin Ƙwaya Ne

9 hours ago
Next Post
Yajin aiki

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Tsayin Daka Kan Daidaita Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Siyasa Da Diflomasiyya

Sin Ta Yi Tsayin Daka Kan Daidaita Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Siyasa Da Diflomasiyya

July 21, 2025
Mutumin El-Rufai, Baloni, Ya Fice Daga APC A Kaduna

Mutumin El-Rufai, Baloni, Ya Fice Daga APC A Kaduna

July 21, 2025
An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari

An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari

July 21, 2025
Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro

Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro

July 21, 2025
Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja

Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja

July 21, 2025
Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015

Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015

July 21, 2025
Ƴan Bindiga Sun Tafka Gagarumar Sata A Bauchi, Sun Tafi Da Mutane 4

Ƴan Bindiga Sun Tafka Gagarumar Sata A Bauchi, Sun Tafi Da Mutane 4

July 21, 2025
Yadda Gwamnan Katsina Ya Tsira Daga Hatsarin Mota

Yadda Gwamnan Katsina Ya Tsira Daga Hatsarin Mota

July 21, 2025
Saurayi Ya Kashe Budurwarsa, Yace Sharrin Ƙwaya Ne

Saurayi Ya Kashe Budurwarsa, Yace Sharrin Ƙwaya Ne

July 21, 2025
Kamfanonin Kera Kayan Likitanci Na Duniya: Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Kasar Sin Babban Ginshiki Ne

Kamfanonin Kera Kayan Likitanci Na Duniya: Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Kasar Sin Babban Ginshiki Ne

July 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.