Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen karbo wasu jiragen yaki 24 daga kamfanin kere-kere na Leonardo da ke kasar Italiya.
Kakakin rundunar sojin saman Nigeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa.
- Hauhawar Farashi Ta Sake Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Cikin Talauci – Bankin Duniya
- A Watan Mayu Za A Bude Bikin Baje Kolin Motoci Na Afrika A Legas
Cikin sanarwar da Gabkwet ya fitar, ya ce ana sa ran karban jiragen yakin kirar M-346 nan ba da jimawa ba, kuma kafin karshen shekarar 2024 kashin farko da adadi shida na jiragen za su isa Nijeriya.
Sanarwar na zuwa ne bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban kamfanin na Leonardo, Claudio Sabatino ya kai wa babban hafsan sojin saman Nijeriya a ranar Laraba, inda ya ce kamfanin zai shafe tsawon shekaru 25 yana kula da jiragen kamar yadda bangarorin biyu suka kulla yarjejeniya.
Wannan wani mataki ne da gwamnatin tarayya ke shirin dauka na ci gaba da yaki da ‘yan bindiga da ‘yan tada kayar baya na Boko Haram a Arewa Maso Gabas.