Wani makiyayi da shanu akalla 12 ne rahotanni suka ce tsawa ta kashe a Kudancin Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi a Matuak Giwa, gundumar Bondon, masarautar Moro’a a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
- Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar
- Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
A cewar Hakimin Kauyen Matuak Giwa, Simon Ayuba, matashin makiyayin ya fake wa ruwan sama ne ajikin bishiya tare da shanunsa lokacin da tsawar ta afka musu, inda nan take suka mutu.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Malam Tanko Isiyaka, shugaban fulani na gundumar Bondon, ya bayyana cewa marigayin ya fito ne daga jihar Bauchi.
Ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin tare da yin kira da a yi addu’a tare da tallafa wa iyalan mamacin. An yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp