Tsawa ta yi sanadin rasuwar wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwar da mutane ne a yankin Oro- Ago da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin data gabata, wani faifan bidiyo d ya karade kafafen sada zumunta, ya nuna inda wasu mutum uku wadanda ake zargin suna daga cikin masu garkuwar da mutane takwas da suka kai wani hari a yankin Iwo na jihar Osun a makwanni uku da suka gabata.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Yi Wa Jama’a Kutse A Asusun Banki
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 7 Da Ceto Wani Mutum A Afganistan
Faifan bidiyon ya nuna yadda gawarsu ta fara rubewa, wadanda tuni, aka banka masu wuta a cikin wani daji.
Kazalika, an ji sautin wata murya cikin faifan bidiyon ana cewa, “ Mu mambobin kungiyar sintiri ne da ke yankin Igbomina na jihar Kwara, kuma hakarmu, ta fara cimma Ruwa kan masu kawo mana hari.”
Wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Adelesi, ya tabbatar da faruwar lamarin, rundunar kuma ta fara gudanar da bincikenta a kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp