Bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro El Mokhtar Sissoco Embalo, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin tun daga gobe Talata 9 zuwa Asabar 13 ga watan nan.
Game da ziyarar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya bayyana yakininsa cewa, ziyarar za ta sanya sabon karfi ga zurfafa dangantakar kasashen biyu, da kara ciyar da hadin-gwiwarsu gaba.
Jami’in ya kuma ce, a yayin ziyarar, shugaba Xi zai shirya wa takwaran nasa na Guinea Bissau bikin maraba da zuwa gami da liyafa, kana kuma za su gudanar da shawarwari. Kaza lika shi ma firaministan kasar Sin Li Qiang, zai gana da shugaba Embalo. (Murtala Zhang)