Tsohon Babban Alkalin Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Mohammed Uwais, ya rasu yana da shekaru 89. Rahotanni daga cikin iyalinsa sun tabbatar da rasuwarsa a safiyar Juma’a, 6 ga Yuni, 2025, a birnin Abuja.
An fara shirye-shiryen gudanar da Sallar jana’iza da binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An haifi Mohammed Uwais a ranar 12 ga Yuni, 1936. Ya riƙe muƙamin babban Alƙalin Nijeriya daga shekarar 1995 zuwa lokacin ritayarsa a 2006.
Bayan ya bar aikin kotu, marigayi Uwais ya shugabanci kwamitin gyaran dokar zaɓe a lokacin Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin zaɓe a ƙasar a Nijeriya.
A ƙarƙashin jagorancinsa ne aka fitar da rahoton gyaran zaɓen da ya janyo hankalin ƙasa da ƙasa, wanda har yanzu ake nazari da amfani da shi wajen ci gaban tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Allah ya jikansa da rahama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp