Tsohon Babban Sufeton ‘Yan-sandan Nijeriya, Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu bayan wata gajeruwar jinya a Lagos, yana da shekara 74.
BBC ta rawaito, Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata kafa daga iyalansa ta tabbatar mata cewa ya rasu ne a yau Alhamis da misalin karfe 8:30 na daren nan a wani asibiti da ke Lekki a Jihar Lagos bayan wata gajeruwar jinya.
- Gwamnatin Benuwai Ta Kafa Rundunar Tsaro Don Fatattakar ‘Yan Bindiga A Jihar
- 2023: APC Ta Ayyana Gwamna Lalong A Matsayin Daraktan Yakin Kamfen Din Tinubu
Balogun wanda aka haifa a ranar 8 ga watan Agusta na 1947 a garin Ila-Orangun da ke jihar Osun, shi ne Shugaban Rundunar ‘Yan-sandan Nijeriya na 21 a tarihi, bayan da aka nada shi a makumin a watan Maris na 2002.
Kafin ya kai wannan matsayi ya rike mukamai da dama da suka hada da mukaddashin kwamishinan ‘yan-sanda a JIhar Edo.
Ya kasance da Kwamishinan ‘yan-sanda na farko na Jihar Delta. Ya kasance Kwamishinan ‘yan-sanda na jihar Ribas da kuma Jihar Abia.
Bayan da ya samu karamin mukami zuwa mataimakin babban sufeton ‘yan-sanda mai kula da shiyya ta daya aSure to Kano, daga nan ne likkafarsa ta yi gaba inda aka nada shi Sufeto Janar din a ranar 6 ga watan Maris na 2002.
A ranar 4 ga watan Afrilu na 2005 hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati EFCC ta gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kan zargin sata da halatta kudaden haram sama da dala miliyan 100 a tsawon shekara uku da ya yi a mukamin Sufeto-Janar.
Hukumar ta EFCC karkashin jagorancin Nuhu Ribadu ta tuhume shi da laifuka 70, inda daga bisani ya yi yarjejeniya ta bayar da wasu daga cikin kudade da abuibuwan da ake zarginsa da sace wa domin a sassauta masa, inda aka yanke masa hukuncin wata shida a gidan yari.
Mai shari’a Binta Nyako ta zartar da cewa kasancewar ya nuna nadama kuma wannan shi ne lokaci na farko da ya aikata laifi ta sassauta masa hukunci.
Ta umarci da ya biya Naira dubu 500 a kan kowanne daga cikin laifuka takwas da ya amince ya aikata daga cikin 56 da suka shafe shi kai tsaye, tarar da ta kama jumulla Naira miliyan 4.
Mai shariar ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata shida a kan kowanne daga cikin laifukan 8, wadanda zai yi su tare.
Shariar tasa ta dauki hankali inda a wani lokaci ya fadi a kujerar da ya ke a ranar 29 ga watan Yuni na 2005 a kotun.
An sake shi a ranar 9 ga watan fabrairu na 2006 bayan da ya kammala wa’adin, wani daga ciki a babban asibitin kasa na Abuja.