A yau Juma’a, kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar, da majalisar gudanarwa ta kasar, tare da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, sun fitar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka sanar da cewa, Li Keqiang, mamban kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin koli na 17 da na 18 da na 19 na Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin (JKS), kana tsohon firaministan kasar Sin ya rasu a yau Juma’a a birnin Shanghai, yana da shekaru 68.
Li ya rasu ne sakamakon zuciyarsa da ta buga da misalin karfe 12 da mintuna 10 na safiyar yau Juma’a bayan da duk wani yunkuri na farfado da shi ya ci tura, a cewar sanarwar.
Li ya samu daukaka a matsayin fitaccen mamba na JKS, jajirtaccen dan kwaminisanci mai aminci da ya jure zamani, kuma fitaccen dan gwagwarmayar juyin juya hali, jigo kuma jagoran jam’iyyar da kasar. (Muhammed Yahaya)