Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammad Sanusi S. Kiru, ya soki gwamnatin jihar bisa matakin sauya wa Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta ’Yan Mata (GGSS) Maikwatashi zuwa unguwar Kaura Goje.
A cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kiru, ya ce matakin bai shi da tsari kuma ya jefa ɗalibai, malamai da al’umma cikin matsala.
- An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
- Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
Ya ce tashin tsohuwar makarantar kafin kammala ginin sabuwar makarantar ya nuna rashin ƙwarewa da rashin kyakkyawan shiri.
Kiru, ya kuma soki iƙirarin da wasu suka yi na cewa yankin Sabon Gari, inda makarantar ta ke ya zama wajen masu aikata laifi, inda ya bayyana cewa hakan bai dace ga al’ummar da ke goyon bayan gwamnati tun da daɗewa.
Haka kuma, ya zargi cewa an sayar da filin makarantar da aka rushe kimanin Naira miliyan 100 kowanne fili, abin da ya kira asara ga jama’a.
Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi.
Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman a harkokin ilimi da suka shafi jin daɗin dalibai da al’umma.














