Iyalan dan kwallon kafar Nijeriya sun wayi gari cikin makokin rasuwar tsohon kocin Super Falcons, Ismaila Mabo.
Dan uwan Mabo, Injiniya Mansir Salihu Nakande, ya tabbatar da labarin rasuwar a safiyar Litinin yana mai cewa: “Mutuwar babban yayanmu, Ismaila Mabo, ya rasu a safiyar yau Litinin, bayan doguwar jinya.”
Marigayi Koci Mabo ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.
Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau Litinin.