Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Arch Audu Sule Katagum da Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Sanata Halliru Dauda Jika sun fice daga jam’iyyar APC.
Sule da Jika dai sun sanar da ficewarsu daga APC ne a ranar Lahadi, inda suka ce kafin daukan wannan matakin sun tuntubi magoya bayansu da masu ruwa da tsaki, inda suka amince musu da hakan.
- Martani: ‘Ni Dan Kabilar Igbo Ne, Babu Mai Fitar Da Ni Daga Cikinsu’ —Okowa
- Mai Damfara Da Sunan Mace A Facebook Ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano
A sanarwar da Sule ya fitar tare da aike ta ga shugaban APC na Jihar Bauchi da na shiyyar Arewa gami da aike da kwafinta wa shugaban APC na Karamar Hukumar Katagum, ya ce ya bada gudunmawarsa sosai wajen samun nasarar jam’iyyar har ma ya yi aiki a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar da mataimakin gwamnan a karkashin mulkin gwamna Muhammad Abubakar, amma daga yanzu ya bar jam’iyyar.
Kazalika, shi ma Sanata Jika wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin ‘yan sandan a Majalisar Dattawa, ya ce ficewarsa daga APC ya yi ne domin ra’ayin dumbin magoya bayansa.
“Bayan tuntubar abokaina a bangaren siyasa, ina sanar da shugabannin jam’iyyar APC cewa na ajiye katin shaidar zamana dan APC nan take.”
Shi dai Jika ya shiga an dama da shi wajen neman tikitin tsayawa takarar gwamna a Jihar Bauchi a APC, amma Saddique Baba Abubakar ya kayar da shi tare da abokan hamayyarsa.