Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung, ya shiga zanga-zangar nuna rashin goyon baya da tsadar rayuwa a Jos, Jihar Filato, a yau Alhamis.
Dubban mutane sun taru a mararrabar gadar sama don yin tattaki zuwa tsohon shatale-talen filin sauka da tashin jirage kusa da NASCO, suna kira da a kawo ƙarshen rashin adalci a Nijeriya.
- Bata-gari Sun Cinna Wa Sabon Ofishin NCC Wuta A Kano
- An Tarwatsa Masu Zanga-zanga Kan Kokarin Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnatin Kano
Dalung, ya yi kira ga jami’an tsaro da kada su tsorata masu zanga-zangar, yana mai bayyana cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayar da damar zanga-zangar lumana.
Dalung, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, ya jaddada matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta yana kuma kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don magance ƙalubalen ƙasar.
Ya yi nuni da muhimmancin ɗaukar mataki don rage wahalar da jama’a ke sha.
Masu zanga-zangar sun ɗauki kwalaye da rubutattun saƙonni kamar “Muna buƙatar tsaro a Nijeriya da darajarta rayuka,” da “Muna buƙatar kyawawan hanyoyi a karkara da birane a Nijeriya” suna ma su miƙa koken su ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu.