Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.
Lamorde ya rasu yana da shekaru 61 a duniya.
- Ministan Kudin Zimbabwe Ya Jinjinawa Gudummawar Masu Zuba Jari Daga Sin
- Shugabar IMF: Kokarin Zurfafa Gyare-gyare A Kasar Sin Zai Haifar Da Karin Ci Gaban Tattalin Arzikinta
Wata majiya daga iyalansa ta ce, Lamorde ya rasu ne a Masar (Egypt) a ranar Lahadi inda yake jinya
An haife shi a ranar 20 ga Disamba 1962, Lamorde ya kuma shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986 kuma ya yi ritaya a matsayin mataimakin babban sufeton ‘yansanda a shekarar 2021.
Lamorde ya rike mukamin shugaban hukumar EFCC tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Lamorde shi ne Shugaban Hukumar na uku. An nada shi a matsayin shugaban hukumar a ranar 3 ga watan Nuwamba 2011 bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya tsige Farida Waziri. Majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar na uku a ranar 15 ga Fabrairu 2012.
Lamorde, an haife shi ne a ranar 20 ga Disamba 1962 a Mubi, Jihar Adamawa, ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin ilimin zamantakewa a shekarar 1984. Ya shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986.