Tsohon shugaban karamar hukumar Ngaski na Jihar Kebbi, Garba Hassan Warra ya samun ‘yanci bayan ya shafe makonni uku a hannun ‘yan bindiga.
An yi garkuwa da Garba Hassan Warra ne a kan hanyar Tegina-Zungeru akan hanyarsa ta zuwa Abuja.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Bala
- Zan Tabbatar Da Ayyukan Sarakuna A Tsarin Mulki – Tinubu
A cewar wasu majiyoyi, Warra, an ce yana tafiya ne da motarsa, tare da direbansa sai daga baya ya shiga motar kasuwa sannan ya umarci direban nasa ya koma gida.
An tattaro cewa, motar kasuwar da Garba Hassan Warra da ya shiga tare da wasu fasinjoji ‘yan bindiga ne suka kai musu farmaki, inda suka tasa keyarsu zuwa cikin daji.
Haka kuma tun lokacin Garba Hassan yana hannun ‘yan bindigar har tsawon makonni uku kafin daga bisa aka hango Garba Hassan Warra a Kotagora, a Jihar Neja a ranar Juma’a kan hanyarsu da dawo wa gida tare da wasu ‘yan uwansa guda biyu, inda suka karbo shi daga hannun ‘yan bindigar.
A cikin takaitacciyar ganawa da Garba Hassan Warra ta Kai tsaye ya ce “ba zai iya cewa komai ba a yanzu har sai hankali ya kwanta.
“Haka kuma a lokacin hada wannan rahoto ba a tabbatar da ko ya biya kudin fansa ko kuma jami’an tsaro ne suka ceto shi”.