A ranar Juma’a ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tashi daga filin jirgin saman Abuja zuwa Nairobi ta kasar Kenya don jagorantar tawagar masu sa ido a zaben da za a gudanar a kasar ranar 9 ga watan Agusta.
Jonathan zai shugabanci kakkarfar tawagar masu sanya idon ne a karkashin cibiyar ‘Electoral Institute for Democracy in Africa (EISA) don kula da yadda za a gudanar da zaben na kasar Kenya.
- Matsalolin Da Nijeriya Ke Fuskanta Yanzu Ya Zarce Na 2015 Kafin Zuwan Buhari – Sanusi L’Amour
- Bayan Shafe Shekaru 7 Yana Adawa Da Zaben Buhari, Karshe Dai Orubebe Ya Koma APC
Jami’in watsa labarai na tsohon shugaban kasar, Mista Ikechukwu Eze, ya sanar da haka a takardar da ya sanya wa hannu a Abuja ranar Juma’a, ya ce, tawagar ta kunshi mutum 21 daga kungiyoyi masu zaman kansu daga sassan duniya.
Kungiyar zata yi aikinta ne tare da la’akari da dokokin shekarar 2002 na kungiyar OAU da AU na kula da yadda ake gudanar da zabe a Afrika.
Ya kuma kara da cewa, ana sa ran tawagar za ta mika rahotanta na yadda aka gudanmar da zaben a ranar 11 ga watan Agusta.