Zamani mai yayi, zamani mai lokaci, kamar dai yadda a yanzu zamanin ya sauya tunanin mafiya yawan masu lokaci.
Ko wanne mako shafin Taskira yakan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi rayuwar al’umma na yau da kullum, ciki kuma har da abin da ya shafi zamantakewar ma’aurata. Inda a yau tsokacin mu zai yi duba ne game da Matan Aure masu rawa a kafafen Sada zumunta/Yada Labarai a shafukan walwalar jama’a (Social Media), kamar su; Tiktok, Facebook, Instagram, da dai sauransu.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas
Idan aka yi duba da yawan matan Auren da ke kara fantsama a shafukan intanet ta hanyar baje kolin basirar rawarsu, dan ganin an dama da su a fannin raye-raye, za a ga a kullum karuwa suke madadin a ce suna raguwa.
Ko me hakan yake nuni ga macen da take hakan, cinyewa ko wayewa, ko birgewa ko makamancin hakan? Ko suna kallon goben yaransu, ya tarbiyyarsu za ta kasance?, Ko mece ce riba ko alfano game da hakan?, Idan matarka ce ko ‘Yar uwarki ce ta kusa wanne mataki za a dauka?, Wannan ya sa shafin Taskira ya ji ta bakin mabiyansa game da wannan matsala, ga kuma ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Sai dai in ce Innalilahi wa innalaihir raju’un, domin abin ya kazanta matuka, ina rasa mene ne ribar su na fitowa ‘Social Media’ suna rawa, eh! su a ganinsu burgewa ce, amman a zahiri suna nunawa duniya ba su da manya ne a gidansu. Duk cikin zuri’arsu babu wadda suke shakka bare kunya, matar auren ko da ka ganta tana rawan ‘Tiktok’ to auren an yi shi ne na jeka nayi ka, in da ace auren arziki ne idan tafi karfin iyayenta ba za ta fi karfin mijin da danginsa ba. Kuma abin da zai tabbatar da auren na je ka nayi ka ne; wasu sai ka ga har da mijin nasu, mace na rawa mijin na mata liki, alamar shi ma bai da mafadi bare tarbiyya, ta ya ya za mu yi tunanin za su bawa yaransu tarbiyya?, mutumin da ba shi da tarbiyya a ina zai samu ya bawa yaransa, duk matar da ba ta tuna gobenta ba ta ‘Ya’ya za ta tuna goben yaranta. Shawarata garesu su dinga tunawa cewa ko wacce rana za su iya mutuwa, kuma ba za a fasa ganin bidiyoyin ba, ko bayan mutuwar su. Idan babu mutuwa yaransu za su taso su gani, har su rakansu ma, sai ya zama kin gama sharholiyar ba za ki barwa yara abun fadi da zai sa su takaici har bayan mutuwarki. Dan haka ko da yaushe kiyi kokari ki ga kin barwa yaranki da danginki abin da za su yi alfahari da shi ba na tir ba.
Sunana Hadiza D. Auta daga Jihar Zamfara:
Hakikanin gaskiya rawar Tiktok abu ne mai munin gaske, irin wanda ba za a gano illar abin ba har sai tsufa ya fara yin sallama. Domin a lokacin da aka tara diya da jikoki, idan aka ce a fiddo wadannan ‘bideos’ din a gaban iyali. Za a sha kunya kuma za a yi da-na-sanin me ya sa aka aikata. Masu yin hakan suna yi ne a matsayin wayewa, sai dai sun jahilci kansu kuma suna yaudarar raunanniyar zuciyarsu, kuma sun batawa kansu lokaci a banza. Saboda duk wayewar da babu addini cikinta a aikace, to babu wata riba a sai tabewa. Ba su kallon kalar tarbiyar da za su bai wa yaransu a gaba gaskiya, don da suna tunawa da hakan da su daina ko don bayansu, domin ba za su so su aikata kamar yadda suka yi ba. Amma da yake gabansu kawai suke kallo, ba sa takaicin abin da zai janyo wa ‘ya’yansu gori, balle jikokinsu idan tafiya ta mika, ko kuma idan sun mutu su bar baya da kura. Shawarata a nan gare su ita ce, su ji tsoron Allah su daina abin da suke yi, domin duniya ba matabbata ce ba, balle ka sa ran za ka samu damar tuba daga baya, idan ka gama shashanci. Saboda mutuwa tana zuwa koyaushe ba tare da ta kwankwasa wa kowa kofa ba.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Abin da zan ce game da matan Aure masu rawa a ‘Social Media’ ba su san darajar Aure ba, kuma ba sa martaba shi, dan shi aure daraja ce da shi mai tarin yawa, dan sunnah ce ta shugaban hallita Annabi Muhammad (S.A.W), bai kamata a kawo wani abun sabo a cikinsa ba. Idan ni ne zan dauki mataki mai tsauri kamar hana yin ‘Socail Media’ da dai sauransu. Hakan ya nuna cewa ba ta da cikakiyar tarbiyya, kuma wanan yana nuna ma ba ka auri mata mai tarbiyya ba, kuma ta gari, kuma ba za su iya bawa yaransu tarbiyya ba, dan yarana za su dauko irin halayansu, shiyasa ake san buncike kafin ayi Aure. Shawar ta a nan ita ce su ji tsoran Allah, su daina, dan gidan Aure ba wajen wasa bane wajen ibada ne, su yi kokari su nemi Aljannar su Na gode.
Sunana Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
Wannan wata matsala ce da ta zama ruwan dare, babu abin da zan ce sai Allah ya shirya. Gaskiya babu dadi in hangi wata ‘Yar uwata ta jini ko wacce dangantarkar musulunci ta hada mu, in ci karo da bidiyonta a matsayinta na mace mai daraja, tana tikar rawa kamar dai wata sabon kamun hauka, idan ‘yar uwata ce zan nuna mata wannan abin fa da take yi bai dace ba, bai kamaceta ba, sannan ba halin tarbiyya ba ne, idan ma ban santa ba zan shiga ‘commnt sec.’ na ta in fadi mata gaskiya idan kunne ya ji jiki ya tsira. Abin da hakan ke nuna wa kai tsaye rashin tarbiyya da kauyanci, wannan sam! ba wayewa ba ce, domin macen da ta waye ita ce mai killace jikinta da kanta kamar yadda ake boye suturu a taska. Mace ta gari makaranta ce mai zaman kanta dake wanzar da tarbiyya, to haka mace mara tarbiyya za ta kasance uwa mai rushe rayuwar yaranta. Saboda in da shanuwar gaba ta sha ruwa ta baya can za ta, yadda uwar su ke yi su ma haka za su yi. Shawarata gare su su ji tsoron Allah su daina, su sani duk abubuwan nan da suke yi ko bayan ransu za su ci gaba da yawo a ‘media’, don haka a daina babu kyau a addini dama al’ada ta Malam Bahaushe. Mace da kunya da kamun kai aka santa, musamman matar aure, ba girma da mutunci ba ne kina rawa wai ke kin waye ko dai kin hauka ce.
Sunana Masa’ud Saleh Dokadawa:
A gaskiya wannan sabuwar dabi’ar da mata suka dauko tayin rawa kafafen sada zumunta na yanar gizo, ba karamin illa gare shi ba. Rusa tarbiyya, koya wa yara rashin kunya ne, bayan haka cin zarafin al’adar Malam Bahaushe ne. Ba wayewa ba ce, ba cinyewa bane, ba kuma burgewa bane. Hakan yana nuni da cewa macen mara tarbiyya ce, ma munya ce, mara addini ce, mara da’a ce, mara fatan zama uwa ta gari ce. Yadda tarbiyyar yaransu za ta kasance shi ne; gurbatacciya, lalatacciya, in ba an yi da gaske ba ba za a shawo kan abin ba. Sannan ta gama zubar da kimarta a fuskar ‘ya’yanta, gobensu ba za ta yi nisa da daraja ba, saboda uwarsu ta sayar musu da mutunci, kima da daraja. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina, su tuna cewa rusa tarbiyyar ‘ya’yansu suke yi, da kuma ‘ya’yan al’umma baki daya. Mazajensu kuma su hana su yin amfani da wannan kafofin sada zumuntar, iyaye Maza da yayyen ‘yan matan da suke yin wannan dabi’a su saka musu tsauraran matakai akan barin yin hakan, don laifi ne bakaramiba. Malamai su ci gaba da nasiha, jan hankali, da tsoratarwa akan hukuncin wanda ya aikata wannan laifin ranar gobe, suma iyaye su juri yin addu’a ko da yaushe don shiriyar ‘ya’yansu.
Sunana Hassana Hussain Malami (Haseenan Masoya):
A gaskiya wannan ba wayewa ba ce, mace ta fito tana raye-raye a ‘Social Media’. Na daya mutane za su dauketa a marar tarbiyya ko da kuwa iyayenta suna iya bakin kokarinsu za a rinka nuna ‘Yan uwana, ana musu kallon marasa tarbiyya su ma, sannan ita mace da kunya aka santa, amma kin fito kin nunawa duniya ke ba ki da ita, gaskiya hakan ba dai-dai bane. Sannan ni shawarar da zan iya bawa masu irin wannan hali da suyi kokari su daina, sabida gaba ake ji watarana ‘ya’yanki idan suka yi girma za su gani, kuma ransu ba zai yi dadi ba, za a rinka yi musu gori, wannan abun ba dai-dai bane.Tom ina mai bada shawara ga masu irin wadannan munanan hali da su daina ko don gobensu tayi kyau,
Sunana Safiyya Mustapha Mu’az daga Gurin Gawa:
Gaskiya rashin tarbiyya ce da kuma rashin Ilimin addini, sannan kuma babu me laifi face mijinta da ya zuba mata idanu take yin abin da ta ga dama, dan a yanzu babu laifin iyayenta tun da ta fita daga hannunsu, kuma wallahi hakan yana nuni cewa mijinta baya kishinta, sannan kuma tana nunawa duniya cewa tafi karfin mijinta da kuma iyayenta. Ni idan har ‘yar uwata ce zan zaunar da ita nayi mata nasiha sosai, ko da ace gaba take da ni sa’annan kuma idan ba ta ji ba za mu zauna da ‘yan uwana, da iyayena mu yi ‘Meeting’ akanta cewa; tun da an yi mata magana taki ji to kowa ya fita harkarta ko gidanta, a daina zuwa har sai ta gane kuskurenta. Idan ta shiryu sai mu koma mu amala da ita. Ba wata wayewa wallahi idan ma wayewa ce da akwai mata dadama da suka fita wayewar, kuma basa wannan banzan halin, kawai dai wannan rashin hankali ne, da kuma rashin Ilimi. To batun tarbiyyar yaransu ba daga nan take ba, wasu za ka samu iyaye ba su da tarbiyya amma kuma sai Allah ya basu ‘ya’ya masu hankali, babu Inda Allah bai yin ikonsa, inda Matsalar take wajan neman Auran ‘ya’yan. Auran ‘ya’yansu sabida da zarar saurayi ya zo neman Auran yarinya za a fara tararsa da rashin kamun kan Uwarta, sannan kuma ace ai uwar yarinyar shedaniya ce, tafi karfin Mijinta, abin da ta ga dama shi take yi, kai ma babu shakka idan har ka sake ka auri wannan yarinyar haka za ta yi maka, daga nan kuma ta fara jefa yaranta cikin matsala. Shawarata anan ga masu wannan dab’iar suyi kokari su zauna su yi karatun ta nutsu, su duba goben ‘ya’yansu, sannan kuma su tuba su koma ga Allah sa’annan su nemi yafiyar mijinsu.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi daga Jihar Kano:
‘Social Media is a lifestyle’ ba wani Abu bane ga wada ta kare tarbiyyar ta. Gani suke cinyewa ne. Tarbiyyar wannan ta Allah ce sai ka ga uwar banza, yaro kuma nagari. Dan Allah su gyara ko da goben yaranmu.
Sunana Amina Mu’awuya Mukhtar:
Abun kunya ne a tare da duk wani wanda ya san daraja da mutunchin kansa, a matsayinki na uwa kuma madubi ga zuri’arki, matakin da zan fara dauka shi ne; zan fuskance ta na fada mata gaskiyar al’amarin da take aikatawa domin kuwa wannan ba hanya ce me bullewa ba, idan taki yadda to ba zan taba bari a san alakata da ita ba, domin wannan ba abun alfahari bane, abun kunya ne. Babu wasu alamun wayewa, cinyewa ko kuma birgewa ga matar auren da take rawa a ‘Social Media’ ba, hakan yana nuni da cewa bata san daraja, kima da kuma mutuncin kanta ba, sannan ba za ta iya bawa ‘ya’yanta nagartacciyar tarbiyya ba. Mawuyaci ne su samu nagartacciyar tarbiyya, domin ita ma babu balle ta basu, basa kallon goben yaransu da suna kallo ba za su yi abin da suke yi ba. Ki ji tsoron Allah ki tuna cewa mace uwa ce ba ga ‘ya’yanta ba ma, hatta ga al’umma kuma ita din madubi ce abar dubawa ga ‘ya’yenta.
Sunana Fatima Jaafar Abbas daga Jihar Kano Rimin Gado:
Gaskiya rawa a ‘Social Media’ ba abu bane mai kyau, don rashin kunya ce, sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce “kunya na daga Imani”, matakin da za a dauka shi ne; iyaye, da mazaje, yayye, da malamai su ci gaba da nunawa matasanmu musamman Mata hakan babu kyau, malamai su ci gaba da fadakarwa. Hakan baya nufin wayewa domin addin musulunci shi ne addinin wayayyu matukar kana so ka waye to kabi dokokinsa kin bi kuma jahilci da kauyanci. Gaskiya basa kallon goben yaransu da tarbiyyarsu, domin ‘ya’yansu ba za su zama masu alfahari da iyayensu ba, domin suma tarbiyyar bata ishe su ba. Su ji tsoron Allah, su daina rashin kunya da raye-raye, domin hakan ba tarbiyyar musulma ba ce.