Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa Jumma’ar nan cewa, kasar Sin na fatan Amurka za ta yi wani gamsasshen bayani game da rahoton baya-bayan nan da aka fitar na cewa, Amurka ce ta tsara harin da a kaiwa bututun jigilar iskar gas na “Nord Stream”, don haka ta gaggauta ba da amsa yadda ya kamata ga galibin tambayoyin da al’ummar duniya ke yi kan wannan batu.
Dangane da nazari da bincike kan balan-balan kasar Sin da sassan da abin ya shafa na Amurka ke gudanarwa, Wang Wenbin ya yi kakkausar suka kan ‘yancin kai, yin komai a bude da kuma bayyana gaskiya a cikin binciken.
Dangane da sukar da jakadan Amurka a kasar Sin ya yi kan rahoton da kasar Sin ta fitar mai alaka da Amurka kuwa, Wang ya bayyana cewa, Amurka ba ta saba sauraron gaskiya ba, bale ma ta fuskanci matsalolinta.
Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan batun kasar Ukraine, da sa kaimi ga yin shawarwarin zaman lafiya, da taka rawar gani wajen sa kaimi ga warware rikicin.
Dangane da bayanan da kasar Sin ta samu game da zuba jarin kasashen waje a bana, Wang ya ce, wannan “farko ne mai kyau”, wanda ya nuna karara cewa, har yanzu kasar Sin ta kasance wuri mai kyau wajen zuba jari ga kasashen waje, kana ma’aunin tattalin arzikin duniya.
Game da hanyar zamanantar da kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana cewa, hanyar zamantarwa ta kasar Sin, ba kawai za ta taimaka wa ci gaban kasar Sin ba, har ma da ci gaban duniya baki daya. (Mai fassarawa: Ibrahim)