Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zaqulo muku batutuwa waxanda suka shafi al’umma ta fanni daban-daban, inda a yau shafin namu zai yi duba ne game da irin halin wasu mazan, musamman masu zaman majalisa ta yadda suke bayyana sirrin gidajensu, kamar wajen yin cefane da sauransu.
Wasu mazan yayin da suka bayyana a majalisa ba su da aiki face bayyanawa sauran abokai sirrikansu, kamar misali; “Maggin dana siya tare da kai tuni nawa ya qare”, wani kuma ya ce shi gidansa da mai gwangwani xaya ake girki, wani kuwa zai ce yadda azumi ya kama kudin cefanen gidansa naira dari biyu ne babu qari ta ishi gidansa cefane.
- A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d
- Manoman Rani Na Sa Ran Samar Da Shinkafa Da Alkama Mai Yawa A Taraba
Wanda alhalin dukkaninsu da suke tare a wajen ba yawan iyalansu da samunsu daya ba, balle su kwatanta shi ya zamo xaya. Ko mene ne amfanin hakan, kuma me hakan zai iya haifarwa? Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Wannan dabi’a ce mara kyau wacce bai kamata mutane su rinka yinta ba, Musamman mazaje, magidanta, kididdiga akan abin amfanin yau da kullum kamar cefane da sauransu, bai kamata ba har ma abokai su rinka zuga abokanansu akan yadda za su saka ido ga matayensu, wannan ba daidai bane. Ba shida wani amfani, kuma zai haifar da matsaloli kamar yawan rigima tsakanin mata da miji, rashin yadda, mammako da rashin yalwatawa iyali da kuma rashin fahimtar juna tsakaninsu. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su kiyaye hakkokin iyalensu, su sani cewa hakki ne su kyautatawa iyalansu ba wai takurawa ba, don ba musulunci bane yin hakan, sannan malamai su rinka yawaita huduba da nasihohi akan yalwatawa da farantawa iyali, sannan su sani cewa Allah zai tambaye su akan duk nauyin da aka dora musu na iyalensu, sannan su sani cewa ibada ne in suka yi hakan akwai lada babba don ibada ne.
Sunana Abdulrrashid Haruna daga Jihar Kano:
Na’am a zahiri wannan rashin sanin kimar kai ne, da rashin sanin darajar kai,da rashin sirri, da shegen surutu mara amfani wanda a karshe hakan zai zama cin mutunci ga duk mai fadar sirrin iyalinsa. Hakan bai da wata fa’Ida sai dai ma ila da yake da shi, domin duk wanda ya ke ma labe wata ran zai shigo. Shawara shi ne su fahimci rayuwa kan cewa dan guntun gatarinka ya fi sari ka bani, ni da kai akwai bambanci, haka za abincin mu ma ya bambanta, rayuwa sirri ce kuma ciki ba dan tuwo da ruwa aka yi shi ba, Allah ya kyauta.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Gaskiya yawancin mutane haka suke kuma haka ba daidai bane, amma wasu sun maida shi dabi’a. Gaskiya hakan ba shi da wani amfani wanan yana haifar da rabuwar kan iyali, shawarata a nan haka ba daidai bane kuskure ne babba a kiyaye.
Sunana Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Bai dace ba, domin wata kila ba yawan dawainiyar ku daya ba, wani daga cikinshi sai na matarshi. Wani kuma akwai yara, idan babu yara tana iya yiyuwa gidanka ana yawan baki. Kuma adadin man da za a zuba a cikin abinci ya danganta ne da yawan abincin, sannan kowacce mace da yanayin salonta wajen sarrafa abinci, kamar misali wasu matan har yanzu suna amfani da gishiri, wasu kuma da maggi kawai suke amfani, wadda bata amfani da gishiri maginta zai riga karewa, idan ma yawanku daya kenan, a takaice dai babu tsari ka zauna kana irin wannan maganar, saka ido ne kawai irin na wasu mazan, wanda zai iya haifar masu da matsala, dan wani ma ba gaskiya ya fada ba, kawai dai ya kuranta matarshi ne, dan haka rashin wayau ne ka zauna kana nuna matarka na maka barna, zai zama kamar ka nuna gazawarta ne ga abokan ka. Shawarta ga masu aikata irin wannan shi ne; su bari domin hakan kamar suna kushe matan nasu ne a wurin abokai, kuma hakan zai sa abokan suwa matar kallon mabarnaciya, idan ma sun bar zancen a tsakanin su kenan.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi (Dr.haibat) daga Jihar Kano:
Gaskiya iri-irin waannan abun ya kan jawo tashi hankali da zargi dama rashin zaman lafiya tsakani miji da mata, ya kamata maza su san mai za su rinka yin hira a kanshi saboda zaman majalisa ba waje bude sirrin nayi, ba ko me ake fadawa aboki ba ko dan gudu matsala kuma inka kula da matar ka kai ma za ka ji dadi, ka ga matar ka tayi kyau kuna cikin kwanciyar hankali dan Allah ‘yan uwa da abokai, da iyaye mu duk mai yin haka yayi kokarin gyarawa ko dan gobe yaranmu, azumi wata ne me dinbun samun lada, a gaskiya ba wani amfani illa ya jawo maka magan-ganu marasa dadi saboda ita mace ‘yar a kula ce ko da yaushe tana bukatar kulawar mijinta, kalmomi masu dadi, Allah ya sa mu gyara.
Sunana Osman Abdullahi Mustapha (Abba Goma) daga Jihar Kano:
Shawarata anan majalisa fa ba wajen fadin sirri ko wani matsala da kai tsakaninka da matar ka ba gaskiya ‘yan uwa na maza a gaskiya bai kamata ace muke yi wa mata haka ba, ko ba komai in aka dafa kaima za ka ci, yaranka ma haka, hakan ba shi da wani amfani sai ma kawo rashin zaman lafiya wanda zai haifar da da mara ido, kana da kanwa da anti da yaya kila ma a gidanku kai ne namiji, haka kuma ba za ka so ace an yi wa daya daga cikinsu haka, dan Allah muyi kokarin magance matsala.
Sunana Yakubu Obida daga Jihar Kano, Farawa, Karamar Hukumar Ungogo:
Gaskiya abin da ya ke faruwa kuskure ne ga maza har mata ma, dan ba maza ne kadai suke irin wannan abun ba, zai yi wahala ka ga namiji ya fita yana bayyana abun da yake faruwa a gidansa. Gaskiya namijin da ya ke irin wannan abun ba daidai bane tsakani da Allah, ka fito waje kana fadar sirrin gidanka, ko amininka ne gaskiya ba kowanne abu bane za ka fito waje kana fada na sirrin gidanka kuskure ne. Hakan ba shida wani amfani, idan har ka dauka ka kai waje, shi wanda ka je ka fadawa za ka ga sai dai ya dawo yana yi maka gori, ko yana yi wa matan gori, ta kowanne bangare akwai matsala, ta ‘ya mace ne ko da namiji, zubar da kima ne da zubar da darajar aure. Duk wani abu da yake tafiya ba daidai ba idan da san samu ne kamata yayi macen taiwa mijin magana, ko shi ya yi wa macen magana, in abun ya gagara ne sai a kai kara zuwa gidansu mijin, ko kuma shi ya kai kara gidansu macen, ina tunnin wannan ita ce mafita. Amma ka dauki zance ka kai waje bai dace ba zai kawo matsaloli da dama kamar zubar da kima a idon wanda aka je aka fadawa, lokacin da ka sanar da mutum daya shi baka san mutane nawa zai je ya sanarwa ba. Idan kuwa magana ne na iyaye mahaifi da mahaifiya sun san yadda za su yi musu a magance matsalar. Shawarar da zan bawa masu irin wannan halin su daina, dan ba dabi’a ce me kyau ba.