Sarkin Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin man fetur a shekarar 2012 saboda tsoron hare-haren Boko Haram.
Sanusi, wanda a lokacin shi ne Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana hakan ne a taron Oxford Global Think Tank Leadership Conference.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
- Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
Ya ce gwamnatin Jonathan ta ji tsoron cewa cire tallafin zai iya haddasa tarzoma sannan ‘yan ta’adda za su iya amfani da damar wajen kai hari.
Ya bayyana cewa tsarin tallafin man fetur ya jefa Nijeriya wahala mai yawa, domin duk lokacin da farashin mai ya tashi, gwamnati ce ke biya kuɗin.
A cewarsa, hakan ya jawo wa ƙasar ta fara neman bashi har ta kai matakan da ba a so.
Sanusi ya ƙara da cewa da an cire tallafin a shekarar 2012, da talakawa wahala kaɗan za su sha a wancan lokacin.
Haka kuma, ya soki shugabannin Nijeriya, yana cewa da yawa daga cikinsu suna mantawa da nauyin da ya rataya a wuyansu bayan sun hau mulki, suna fifita buƙatunsu maimakon jin daɗin jama’a.














