Jami’in hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA), Yahaya Isma’il Idris, ya rasu bayan faɗowa daga wata mota a safiyar Alhamis a kan titin Maiduguri, cikin birnin Kano.
A cewar Zagazola Makama, wanda ya wallafa sanarwar a shafinsa na X, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na safiyar Alhamis lokacin da jami’in, wanda ke kan aikin dare, ya dakatar da wata mota ɗauke da kaya domin duba takardun zirga-zirga.
- Ganduje Ya Jajantawa Shugaban KAROTA Baffa DanAgundi Sakamakon Rasuwar Mahaifiyarsa
- Tinubu Ya Tabbatar Da Aniyar Gwamnatinsa Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Motar, mai lambar rajista BWR 457 XC, wacce direbanta Yakubu Abdulsalamke tuƙawa, mai shekaru 25 daga ƙaramar hukumar Fika a Jihar Yobe, tare da fasinjoji guda biyu — Tunde Momodu, mai shekaru 31 daga Jihar Edo, da Sagir Yusuf, mai shekaru 21 daga ƙaramar hukumar Bichi a Jihar Kano.
Idris ya buƙaci direban ya nuna takardar kwangilar ɗauko kaya, amma saboda rashin gabatar da takardar, ya hau motar domin ci gaba da bincike. Bayan wani lokaci, direban ya tashi da motar cikin sauri, a yayin da motar ke kusa da gador Muhammadu Buhari Interchange, bangaje jami’in daga cikin motar ya faɗo.
Idris ya samu raunuka masu tsanani kuma an garzaya da shi zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad a Kano, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp