Wasu tubabbun mayakan Boko-Haram sun gudanar shara da tsabtace birnin Maiduguri, yau Asabar a wani yunkuri da gwamnati ke yi na al’uma su sake amince wa da su don ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba.
Cibiyar ci gaban dimukuradiyya (CDC) tare da hadin guiwar gwamnatin jihar Borno sun shirya wani aikin tsabtace muhalli ga tubabbun mayakan Boko Haram suka aiwatar a kwaryar birnin Jihar.
- Sojojin Nijeriya Sun Cafke Masu Kai Wa ‘Yan Boko Haram Kayan Abinci Da Sutturu
- Luguden Ruwan Wuta Ya Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
Da yake bayanin makasudin aikin, Mala Mustafa, babban jami’in gudanar da bincike a cibyar, ya bayyana cewa an bullo da wannan matakin ne a don shirin mayar da tubabbun cikin al’uma don ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba.
“Makasudin da ya sanya CDD ta bai wa gwamnatin jihar Borno goyon baya wajen gudanar da wannan shirin shi n,e domin jama’a su sake karbar tubabbun hannu biyu.”
“Muna da kudurin samun sauyin matsayi da kallon da jama’a suke yi wa sha’anin, musamman kallo mara kyau da al’uma suke da shi a garuruwa daban-daban.”
“Saboda haka muna kokarin sake inganta alaka tsakanin al’uma da tubabbun mayakan a garuruwanmu.” In ji Mustafa.
Ya kuma ya bayyana cewa sun yi amfani da tubabbun mayakan kimanin 400 domin gudanar da aikin tsabtace muhalli tare da wasu 50 cikin wadanda aka fara aikin shara da su a sansanin Alhazai da ke Maiduguri wanda ya kunshi kimanin tubabbun mayakan 12,000 da iyalansu.