- Ba Ma Ganin ‘Yan Siyasa Sai Lokacin Zabe
- Har Yanzu Muna Fuskantar Barazanar Tsaro, In Ji Mazauna Garin
Garin Tudun Biri, da ke Gundumar Afaka a Karamar Hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, wanda ya karade kafafen yada labarai tun daga makon jiya saboda harim bam da sojoji suka kai, gari ne da ya kwashe fiye da shekaru 200 da kafuwa ba tare da samun asibiti ko makarantar boko ba.
Gari ne na manoma da ya kunshi Zallar Hausawa da tsirarun gwarawa mai makwabtaka da filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna amma abin mamaki garin duk da kasancewarsa mafi kusa da filin jiragen saman na Kaduna amma babu abubuwan more rayuwa.
- Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wadanda Ta Yi Wa Rusau Diyyar N3bn
- Al’ummar Tudun Biri Sun Kai Karar Gwamnatin Tarayya Kan Biyan Su Diyya
Wani Dattijo mai shekara 74 a duniya, ya shaida wa wakilinmu cewa, Tudun Biri gari ne mai tsohon tarihi domin hatta kakansa ma a nan aka haife shi, sannan suna zaman lafiya a tsakanin Hausawa da Gwarawa da kuma Fulani da ke yankin.
A wata ziyara da Wakilinmu ya kai garin, wani matashi ya dauke a babur inda suka kewaya garin tare da ganin yadda mazauna kauyen ke rayuwa babu asibiti ko da sha-ka-ta-fi, wutar lantarki ko makarantar boko, duk da cewa suna taka rawar gani wajen zaben shugabanni lokacin zabe.
Duk da cewa galibin mutanen Tudun Biri manoma ne amma ba su da hanyar da idan sun girbe amfanin gona za su fitar zuwa kasuwa ga kuma matsalar rashin tsaro na ‘yan bindiga da suke musu barazana.
Wakilinmu ya tarar da al’ummar garin suna zaman zullumi biyo bayan harin bam na makon jiya. Sai dai ya samu damar tattauawa da wasu mutanen garin. Na farko, wani matashin dattijo, Alhaji Ahmed Adamu, mai shekara 50 da haihuwa.
Ya bayyana cewa, “Kakanninmu a wannan garin aka haife su, haka iyayenmu da mu kanmu duk a wannan garin aka haife mu Amma ni tun da na taso ba mu taba samun Asibiti ba ko dakin shan magani wanda idan muna da mara lafiya babu abin da muke yi sai mu shiga jeji mu sama masa maganin gargajiya idan abin yaki sai mu je Buruku ko mu je Mando domin neman maganin Bature hatta cikin filin jiragen sama na Kaduna babu asibiti.
“Har gobe ba mu da wata hanyar sama wa yaranmu magani wanda ya wuce na gargajiya, idan jikin mara lafiyar bai yi zafi ba, haka nan za mu dauke shi rigin-rigin mu kai Mando ko Buruku domin samun maganin bature. Toh yanzu kila da aka samu wannan iftila’in, kila a gina mana makaranta ko Asibiti.” In ji shi.
Shi ma, Malam Adamu Umar, magidanci a garin na Tudun Biri ya shaida cewa “Ba ma kwadayin barin wannan gari saboda kankanninmu a nan aka haife su saboda idan mun bar garin mutuwa zai yi, haka kuma idan mun bar shi to ina za mu?
“Mun sha kai kokenmu ga gwamnati amma ba a taba waiwayen mu ba saboda ga shi kun zo kun ga yadda garin yake da idonku.
“Ba mu da wutar lantarki; ba mu da hanya ba mu da da makaranta. Mu fa yanzu ta kai ba ma ta wutar lantarki muke ba, mu samu hanyar da za mu rinka bi da makarantun da za mu kai ‘ya’yanmu shi ne muka fi so, yanzu haka ‘ya’yanmu suke tashi babu makaranta. Idan ka ga yaro ya samu ilimi a wannan garin sai dai idan mahaifiyarshi za ta tashi da asuba ta dora masa ruwan wanka sannan a lallaba da shi a mashin rugu-rugu a je a kai shi makaranta a cikin gari, idan aka tashi a dawo da shi.” In ji shi.
Har ila yau, LEADERSHIP HAUSA ta zanta da wasu yaran kauyen da ba su wuce shekaru 12 zuwa 15 ba da haihuwa, inda suka bayyana takaicinsu na rashin zuwa makarantar boko ba duk da cewa tana ba su sha’awa.
Daya daga cikinsu, Umar dan shekara 12 ya ce a halin yanzu makarantar ta kara yi masa nisa saboda “ Babana ya rasu, su kuma duk yayuna an kashe su a wannan abin da ya faru. Babu wanda zai kai ni makaranta.”
Shi ma wani yaro, Muhammadu Jibril ya bayyana cewa, “Ba na zuwa makaranta amma dai na yi tunanin zan fara zuwa sai kuma wannan abun ya faru a garin.”
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa,mafi yawan yaran da suke zuwa aikin gona a garin matasa ne wadanda ba su wuce shekaru 12 zuwa 18 kuma duk ba sa zuwa makarantar boko.
Sun nuna takaicinsu a kan yadda ba sa ganin wasu jami’an gwamnati ko ‘yan siyasa sai lokacin zabe kana suka yi kiran a kawo musu daukin gaggawa.
Wani magidanci, Malam Muhammadu Hamisu Aminu, ya yi kira ga musamman Gwamnatin Tarayya ta samar musu da tsaro a garin inda ya bayyana cewa bayan wannan harin bam da ya jefa su cikin alhini, har yanzu suna da fargabar rashin tsaro a yankin.
Wani abin da aka lura da shi har ila yau a garin na Tudun Biri dai, bayan aukuwar iftila’in harin na bam, kusan duk matan garin da tsofaffi da matasa sun sauya shigarsu inda suke sa tufafi masu kyau mata kuma na amfani da sabbin hijabai.