Fashewar tukunyar iskar gas ta kashe wata mata a Unguwar Tabernacle, Garage Egbe a karamar hukumar Omu-aran Irepodun a Jihar Kwara.
Leadership Hausa ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 10:35 na safe a lokacin da take kokarin fada wa iyalinta abincin.
- Xi Ya Jaddada Sake Farfado Da Yankunan Karkara Yayin Da Ya Ziyarci Shaanxi Da Henan
- Wang Yi Ya Gana Da Jakadan Amurka Dake Kasar Sin
‘Yan kwana-kwana sun iya shawo kan lamarin kan lokaci tare da ceto mijin wanda abin ya shafa wanda shi ma ya makale a lokacin da gobarar ta tashi.
Daga nan aka kai shi asibiti.
Rahotanni sun ce wuraren ginin da gobarar ta shafa sun hada da dakin zama da kicin da kuma wurin cin abinci.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bukaci jama’a musamman mata da su je su koyi amfani iskar gas din girki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp