ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Turai Ta San Ra’ayin Amurka Kan Dangantakar Dake Tsakaninsu

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A kwanakin baya ne, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gama ziyararsa ta kwanaki 3 a kasar Amurka. Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don sa kaimi ga kasar Amurka da ta gyara dokar rage hauhawar farashin kaya bisa la’akari da kamfanonin Turai.

Amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, inda ya koma Turai ta bacin rai, duk da dangantakar dake tsakanin Turai da Amurkar.

  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Ta Fitar Da Rahoton Shekara-Shekara Kan Karfin Sojan Sin Da Nufin Fakewa Wajen Nuna Danniya Ko Babakere A Fannin Soja

Shugaba Macron ya ziyarci Amurka a wannan karo don neman dawo da moriyar Turai. A watan Agusta na bana, shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya sa hannu kan dokar rage hauhawar farashin kaya, inda aka gabatar da matakai da dama, ciki har da samar da kudin rangwame don sa kaimi ga kamfanonin da ke kasar Amurka da su raya fasahohin kera motoci masu amfani da wutar lantarki da sauran fasahohi ba tare da gurbata muhalli ba.

ADVERTISEMENT

Kasashen Turai sun nuna rashin jin dadi da wannan doka, domin a ganinsu, dokar tana kunshe da abubuwan bada kariya ga cinikayya, wadda ta sabawa ka’idojin hukumar WTO, kuma hakan zai tsananta halin da masana’antun samar da kaya na Turai ke game da game da kokarinsu na samar da kayayyaki, da tilastawa rassan kamfanonin Turai kaura zuwa kasar Amurka.

Yayin da shugaba Macron ya isa kasar Amurka a yini na farko, ya fara zargin babbar illar da dokar rage hauhawar farashin kaya ta Amurka ta haifar wa kamfanonin Turai, ya ce za a rasa ayyukan yi da dama a kasar Faransa da ma nahiyar Turai, kuma an dauki matakin ne don daidaita matsalar Amurka tare da kawo illa ga moriyar Turai. Shugaba Macron ya kara da cewa, kasar Faransa tana fatan kasar Amurka za ta dauki Faransa a matsayin abokiya, tare da kara yin mu’amala da juna kan tattalin arziki a tsakanin gabobin tekun Atlantic.

LABARAI MASU NASABA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Game da bukatun da shugaba Macron ya gabatar, shugaba Biden ya ce kasar Amurka ba ta bukatar yin afuwa ga nahiyar Turai, Amurka za ta dan yiwa dokar gyara ne, amma bai yi karin haske ba. Kafofin watsa labarai na kasar Jamus sun bayyana cewa, game da batun moriyar tattalin arziki, kasar Amurka tana kula da moriyarta ce kawai, don haka ya kamata kasashen Turai su san da haka. (Zainab)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
Next Post
Kumbon Shenzhou-14 Ya Sauka Cikin Nasara

Kumbon Shenzhou-14 Ya Sauka Cikin Nasara

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.