Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin.
Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da sojoji.
- Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
- Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau
Kauyukan a cewar dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta yamma a majalisar dokokin jihar, Hon. Aminu Boza ya hada da Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar mai ci, Injiniya Idris Gobir.
Boza ya kuma ce, Turji ya koma da ayyukan ta’addancinsa a yankin gabashin karamar hukumar Isa ta jihar.