Assalamu alaikum, don Allah malam ina da tambaya, shin ya halarta uba ya auri kishiyar ‘yarsa Idan mijinta ya sake ta ko ya rasu?
Wa alaikum assalam. Na’am ya halatta, saboda ba ta cikin mata (15) da Allah Ya HARAMTA a suratun Nisa’i. Sai dai yana daga cikin ka’idojin Shari’a duba maslaha da kuma barin halal don kunya.
Allah ne mafi sani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp