An jima ba a kalli wasa mai zafi da kayatarwa kamar wanda aka buga yau tsakanin Inter Milan da Barcelona a filin wasa na San Siro dake birnin Milan ba, duba da cewar duka kungiyoyin biyu babu kanwar lasa a cikinsu a bangaren taka leda.
Kamar wasan farko yau ma an tashi da ci 3-3 a mintuna 90 na wasan, amma sai alkalin wasa Syzmon Machianik ya bayar da damar sake buga wasu karin mintuna 20 domin a fitar da gwani.
- Tawagar Hafsoshin Sojojin Afirka Ta Ziyarci Kasar Sin
- Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi
A wannan karin mintunan, Inter Milan ta samu damar jefa kwallo a ragar Barcelona ta hannun Davide Fratessi, da haka wasan ya tashi da ci 4-3 wanda ya zama 7-6 a duka wasanni biyu da suka buga a zagayen na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai.
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp