Karamin ministan harkokin wajen kasar Uganda John Mulimba, ya jinjinawa gudummawar da kasar ke bayarwa ga cimma nasarar manufofin wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin kahon Afirka.
John Mulimba, ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa ga mahalarta taron tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiya, da samar da ci gaba a yankin kahon Afirka karo na uku, wanda ya gudana a birnin Kampala fadar mulkin kasar ta Uganda.
- Amurka: “Afirka Ba Ta Cikin Jerin Fannoni Da Muka Ba Da Fifiko A Kai”
- Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
Ya ce har kullum, kasar Sin na mara baya ga shirye-shirye dake mayar da hankali ga gudanar da shawarwari, da warware matsaloli a yankin, musamman a gabar da yankin ke fuskantar tarin kalubale da suka hada da na tsaro, da barazanar tsaron tsakanin iyakokin yankin, da matsalolin muhalli da raunin tattalin arziki.
Cikin jawabin na mista Mulimba, wanda kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu kwafi a jiya Laraba, ta hannu ma’aikatar harkokin wajen Uganda, ya ce a wani mataki mai nasaba da hakan, kasar Sin ta samar da gudummawar shawarar tabbatar da tsaron duniya, wadda ta share fagen tattauna matakan samar da tsaron kasa da kasa na bai daya.
Mulimba, ya ce shawarar ta kasar Sin ta mayar da hankali ga karfafa tattaunawa, da mutunta ikon mulkin kai, da cikakken tsarin warware rigingimu, wanda ya dace da ajandar kungiyar AU ta nan zuwa shekarar 2063, musamman ma burin kasashen Afirka na wanzar da tsaro da zaman lafiya a daukacin nahiyar.
A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp